Lallai masu yawaita tsinuwa ba sa zama masu shaida ko masu ceto a ranar alƙiyama

Lallai masu yawaita tsinuwa ba sa zama masu shaida ko masu ceto a ranar alƙiyama

Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai masu yawaita tsinuwa ba sa zama masu shaida ko masu ceto a ranar alƙiyama".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda yake yawaita tsinuwa akan wanda bai cancanteta ba to shi ya cancanci uƙuba biyu: Ta farko: Ba zai zama mai shaida ba a ranar alƙiyama akan al'ummu na isarwar Manzanninsu ga saƙonni zuwa garesu, kuma ba za'a karɓi shaidarsa ba a duniya; dan fasiƙancinsa, kuma ba za'a azurta shi da shahada ba ita ce mutuwa a tafarkin Allah. Ta biyu: Ba zai yi ceto ba a ranar alƙiyama lokacin da muminai suke yin ceto ga 'yan uwansu waɗanda suka cancanci (shiga) wuta.

فوائد الحديث

Haramta tsinuwa, kuma cewa yawaita ta yana daga manyan zunubai.

Uƙuba a cikin hadisin kawai ita ga wanda tsinuwa ta yawaita daga gare shi ne, badan sau ɗaya ba ko waninsa ba, kuma akwai tsinuwar da ta halatta tana fitowa daga gare shi, shi ne wanda shari'a ta zo da ita da tsinuwar ma'abota siffofi ababen zargi ba tare da ayyanawa ba kamar faɗinka: "Allah Ya la'anci Yahudawa da Nasara", "Tsinuwar Allah ta tabbata akan azzalumai", "Allah Ya tsinewa masu ɗaukar hotuna (yin mutum-mutumi), "Allah Ya tsinewa wanda ya yi aiki irin aikin mutanen (Annabi) Luɗ", "Allah Ya tsinewa wanda ya yi yanka ga wanin Allah", "Allah Ya tsinewa mazan da suke kamanceceniya da mata, da matan da suke kamaceceniya da maza", da makamancin hakan.

Tabbatar da ceton muminai a ranar alƙiyama.

التصنيفات

Munanan Halaye