Ya ku mutane ku yaɗa sallama, ku ciyar da abinci, ku sadar da zumunci, ku yi sallah alhali mutane suna bacci, zaku shiga aljanna cikin aminci

Ya ku mutane ku yaɗa sallama, ku ciyar da abinci, ku sadar da zumunci, ku yi sallah alhali mutane suna bacci, zaku shiga aljanna cikin aminci

Daga Abdullahi ɗan Salam - Allah Ya yarda da shi - ya ce; Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso Madina sai mutane suka fuskanto gare shi, aka ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso, sau uku. Sai na zo a cikin mutane dan inyi kallo, lokacin da na gane fuskarsa, sai nasan cewa fuskarsa ba fuskar maƙaryaci bace, farkon abinda na fara jinsa ya yi magana da shi cewa ya ce: "Ya ku mutane ku yaɗa sallama, ku ciyar da abinci, ku sadar da zumunci, ku yi sallah alhali mutane suna bacci, zaku shiga aljanna cikin aminci".

[Ingantacce ne]

الشرح

Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo Madina, mutane suka ganshi sai suka fuskanci inda yake suna gaggawa, daga waɗanda suka fuskanci inda yake Abdullahi ɗan Salam - Allah Ya yarda da shi - ya kasance daga Yahudawa, lokacin da ya ganshi sai ya san cewa fuskarsa ba fuskar maƙaryaci ba ce; dan abinda ya bayyana gare shi na haske da kyau da kwarjini na gaskiya. Ya kasance farkon abinda ya ji shi daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kwaɗaitar da mutane akan ayyukan da zasu zama sababin shiga aljanna, daga cikinsu: Na farko: Yaɗa gaisuwa da bayyanar da ita da yawaita ta ga wanda ka sani da wanda ma baka sani ba. Na biyu: Ciyar da abinci ta hanyar sadaka da kyauta da tarbar baƙi. Na uku: Sadar da zumunci ga wanda zumunci ko kusanci ya ƙullu tsakaninka da su ta ɓangaren uba ko uwa. Na huɗu: Sallar nafila tsayuwar dare alhali mutane suna bacci.

فوائد الحديث

An so yaɗa gaisuwar sallama tsakanin musulmai, amma wanda ba musulmi ba ba'a fara masa da sallama, idan ya yi sallama da faɗin: Assalamu alaikum, sai a mayar masa da faɗin: Wa'alaikum.

التصنيفات

Tsayuwar Dare, Falalar Ayyuka na qwarai