An ɗauke alƙalami ga mutum uku: Mai Bacci har sai ya farka, da yaro har sai ya balaga, da kuma mahaukaci har sai ya yi hankali

An ɗauke alƙalami ga mutum uku: Mai Bacci har sai ya farka, da yaro har sai ya balaga, da kuma mahaukaci har sai ya yi hankali

Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "An ɗauke alƙalami ga mutum uku: Mai Bacci har sai ya farka, da yaro har sai ya balaga, da kuma mahaukaci har sai ya yi hankali".

[Ingantacce ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin Dora hukunci na (shari'a) wanda yake lazimtar 'ya'yan Adam ne sai waɗannan ukun: Ƙaramin yaro har sai ya girma ya balaga. Da mahaukaci wato mara hankali har sai hankalinsa ya dawo gare shi . Da mai bacci har sai ya farka. Ɗora shari'a haƙiƙa an ɗauke musu ita, kuma aikata laifinsu ba'a rubuta musu, sai dai ana rubuta alheri ga yaro ƙarami banda mahaukaci da mai bacci; domin su suna cikin wadanda ibadarsu ba ta inganta ba daga gare shi saboda gushewar ji.

فوائد الحديث

Rashin cancantar mutum yana zama kodai saboda baccin da rashin farkawa ya sarayar masa da wajibansa, ko saboda ƙarancin shekaru da yarinta wanda hakan ya sa ya rasa cancanta, ko saboda haukan da ayyukansa na hankali suka raurawa tare da shi, ko abinda yake riskarsa kamar maye, wanda ya rasa banbancewa da fayyacewa ingantacciya, to cancanta ta koru daga gare shi saboda sababi daga waɗannan sabubban uku; domin Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - saboda adalcinSa, da haƙurinSa, da kyautarSa, haƙiƙa Ya ɗauke masa kamun abinda yake bijirowa daga gare shi na wuce gona da iri ko gajiyawa a cikin hakkin Allah - Maɗaukakin sarki -.

Rashin rubuta zunubai akansu, ba ya kore tabbatar da hukunce-hukunce na duniya akansu; kamar mahaukaci da zai yi kisa, to babu sakayya akansa kuma babu kaffara, amma akwai diyya akan 'yan uwansa.

Balaga tana da almomi biyar: Fitar maniyyi, ta hanyar mafarki da waninsa, ko tsirowar gashin mara, ko cika shekara goma sha biyar, mace ta ƙara al'amari na huɗu: Shi ne haila.

Al-Subki ya ce: Ƙaramin yaro shi ne yaro.

Waninsa ya ce; Yaro a cikin mahaifyarsa ana ambatansa ɗan tayi, idan aka haife shi to ya zama yaro, idan an yaye shi to ya zama yaro har zuwa shekara bakwai, sannan ya zama mai tasowa har zuwa shekara goma sannan ƙaƙƙarfan yaro, wanda ake yankewa da shi cewa ana ambatansa yaro a cikin waɗannan halayen gaba ɗayansu, Suyuɗine ya faɗe shi.

التصنيفات

Saraxan Sallah