إعدادات العرض
«Kada ku daki bayin Allah mata» sai Umar ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Mata sun yi wa mazajensu tawaye, sai ya yi rangwami a dukansu, sai mata da yawa suka kewaye iyalan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna kawo…
«Kada ku daki bayin Allah mata» sai Umar ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Mata sun yi wa mazajensu tawaye, sai ya yi rangwami a dukansu, sai mata da yawa suka kewaye iyalan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna kawo ƙarar mazajensu, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: @«Haƙiƙa mata da yawa sun kewaye iyalan (Annabi) Muhammad suna kawo ƙarar mazajensu to waɗannan ba zaɓaɓɓunku ba ne».
Daga Abdullahi Dan Iyas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Kada ku daki bayin Allah mata» sai Umar ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Mata sun yi wa mazajensu tawaye, sai ya yi rangwami a dukansu, sai mata da yawa suka kewaye iyalan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna kawo ƙarar mazajensu, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Haƙiƙa mata da yawa sun kewaye iyalan (Annabi) Muhammad suna kawo ƙarar mazajensu to waɗannan ba zaɓaɓɓunku ba ne».
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Kurdî Tiếng Việt Magyar ქართული Kiswahili සිංහල Română অসমীয়া ไทยالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana dukan mata, sai sarkin muminai Umar Ibnu Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya zo kuma ya ce: Ya Manzon Allah mata sun yi wa mazajensu tawaye kuma ɗabi'unsu sun munana. Sai (Manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi rangwami da dukansu dukan da ba zai sa ciwo ba idan an samu sababin yin hakan, kamar idan sun ƙi bada haƙƙin miji da kuma saɓa masa da makamancin haka. Sai wasu mata suka zo a bayansa wurin matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna kawo ƙara akan dukan mazajensu dukan da ba zai sa rauni ba, saboda mummunan aiki da wannan rangwamen, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Waɗannan mazajen waɗanda suke dukan matansu dukan da ba zai sa rauni ba ba zaɓɓɓunku ba ne.فوائد الحديث
Bayanin falalar yin kyakkyawar mu'amala da mata, da kuma yin haƙuri akansu da kau da kai daga abinda yake kasancewa daga gurinsu shi ne ya fi daga dukansu.
Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya sanya ƙarshen matakin maganin taurin kan mata, sai Ya ce: (Waɗanda kuke jin tsoron kangarewarsu, to ku yi musu wa'azi, kuma ku ƙaurace musu a wajen kwanciya, kuma ku dokesu; amma idan sun yi muku ɗa'a, to kada ku nemi wata hanyar cutar da su. Lallai Allah Ya kasance Maɗaukaki ne Mai girma.
[al-Nisa'i: 34].
Kuma wadannan (matakai) ukun a jere suke, ba wai ahaɗe suke a lokaci ɗaya ba, sai ya fara da yin nasiha da wa'azi da gargaɗi idan ya fa'idantar to alhamdu lillah, idan bai amfanar ba sai ya ƙaurace mata a wurin kwanciya, idan bai fa'idantar ba sai ya daketa dukan ladabtarwa ba dukan ɗaukar fansa ba.
Namiji mai kiwo ne a cikin gidansa, dan haka yana wajaba ya tarbiyyantar da su ya kuma tsaftace tarbiyyarsu da hikima da wa'azi mai kyau.
Halaccin nazarin malami a cikin fatawarsa; dan sanin ƙarshenta da kuma makomarta.
Halaccin kai ƙara ga sarki ko malami idan cuta ta riski mai kawo ƙara.