Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci, kuma ba ya kamata gareShi Ya yi bacci

Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci, kuma ba ya kamata gareShi Ya yi bacci

Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu da wasu kalmomi biyar, sai ya ce: «Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci, kuma ba ya kamata gareShi Ya yi bacci, Yana ƙasa da ma'auni kuma Yana ɗaga shi, ana ɗaga aikin dare kafin aikin rana zuwa gare Shi, da aikin rana kafin aikin dare, shamakinSa shi ne haske, da ace zai yaye shi da hasken fuskarSa ya ƙona inda ganinsa ya tiƙe daga halittarSa».

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya yana mai huɗuba a cikin sahabbansa da wasu jumloli biyar cikakku, su ne: Na farko: Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci. Na biyu: Bacci ya koru a cikin haƙƙinSa; saboda cikar ƘayyumiyyarSa da kuma rayuwarSa. Na uku: Allah Yana ƙasa da ma'auni kuma Yana ɗaga shi da abin da ake auna ayyukan bayin da aka ɗaukakasu masu hawa zuwa gareShi, kuma ana aunawa daga arziƙansu masu sauka zuwa ƙasa, arziƙin da shine rabon kowanne abin halitta tsarki ya tabbatar maSa Yana ƙasƙantar da shi sai Ya ƙanƙanta shi, kuma Yana ɗaukaka shi sai Ya yalwata shi. Na huɗu: Ana ɗaga abin da bayi suka aikata da daddare kafin yinin da zai zo a bayansa, da kuma aikinsu da rana kafin daren dake bayansa; Mala'iku masu kiyaye ayyuka suna hawa sama da ayyukan dare bayan ƙarewarsa a farkon yini, kuma suna hawa da ayyukan rana bayan ƙarewarsa a cikin farkon dare. Na biyar: HijabinSa mai hana ganinSa shi ne cikakken haske ko wuta, da zai yaye shi da hasken fuskarSa ya ƙona inda ganinSa ya tiƙe a halittarSa; hasken fuskarSa shi ne haskenSa da kuma ɗaukakarSa da kwarjininSa. Abin ƙaddarawa: Da a ce Ya gusar Ya yaye abin da ke hana ganinSa shine hijabi, Ya yi tajalli ga halittarSa da hasken fuskarSa sun ƙona inda ganinSa ya tiƙe daga halittarSa; sune dukkanin halittu; domin cewa ganinSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - mai kewaye sani ne da dukkanin kasantattu.

فوائد الحديث

Bayanin koruwar bacci ga Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -; saboda kasancewarSa yana daga cikin tauyayyun abubuwa kuma shi abin tsarkakewa ne daga garesu.

Allah - Maɗaukakain sarki - Yana ɗaga wanda Ya so kuma Yana ƙasƙantar da wanda Ya so, Yana shiryar da wanda Ya so Yana ɓatar da wanda Ya so daga cikin bayinSa.

Ana ɗaga ayyuka zuwa ga Allah a kowacce rana da kowane dare, a cikin haka akwai kwaɗaitar da bayi su yi muraƙabar Allah - Mai girma da ɗaukaka - a cikin darensu da kuma yininsu.

Hadisin yana nuni akan adalcin Allah - tsarki ya tabbatar maSa - da kyakkyawan shirya al'amuranSa ga al'amuran halittarSa, babu kokwanto cewa wannan yana daga cikin siffofin cikarSa - Maɗaukakin sarki -.

Tabbatar da shamaki gareShi - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -, shi ne kuma hasken da ya tsare tsakaninSa da tsakanin halittarSa, daban dan shi ba da sun ƙone.

Al’Aajurri ya ce: Lallai ma'abota gaskiya suna siffanta Allah - Mai girma da ɗaukaka - da abinda Ya siffanta kanSa - Mai girma da ɗaukaka - da shi, da kuma abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya siffanta shi da shi, kuma da abinda sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka siffantaShi da shi, wannan (ita ce) mazhabar malamai daga waɗanda ya bi bai yi ƙirƙire ba, Ya ƙare.

Ahlus Sunna suna tabbatarwa Allah abinda Ya tabbatarwa kanSa da shi na sunaye da siffofi ba tare da jirkitawa ko korewa ko kaifantawa ko kamantawa ba, kuma suna korewa Allah abinda Ya korewa kanSa, sunayin shiru daga abinda korewa ko tabbatarwa bai zo da shi ba, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Babu wani abu tamkarSa, Shi ne Mai yawan ji kuma Mai yawan gani}.

Hasken da shi ne siffarSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - ba hasken da Ya shamakantu da shi ba ne, hasken da Ya shamakantu da shi haske ne abin halitta, hasken Allah - Maɗaukakin sarki - haskene daya dace da Shi da kuma zatinSa, babu wani tamkarSa, abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gan shi ba wani abu bane sai shamakin da yake kasancewa tsakanin Allah da bayinSa.

التصنيفات

Tauhidin Sunaye da Siffofi, Falalar Ayyuka na qwarai, Tuba