إعدادات العرض
Da a ce mutum ya yi nufin yin fanɗara alhali shi yana Adan Abyan da Allah Ya ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi
Da a ce mutum ya yi nufin yin fanɗara alhali shi yana Adan Abyan da Allah Ya ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ruwaito shi Marfu'i: A cikin faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Wanda ya nufe shi da wata fanɗara da zalinci zamu ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi} [al-haj: 25] ya ce: "Da a ce mutum ya yi nufin yin fanɗara alhali shi yana Adan Abyan da Allah Ya ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi".
الترجمة
العربية Tiếng Việt Bahasa Indonesia Nederlands Kiswahili অসমীয়া English ગુજરાતી සිංහල Magyar ქართული Românăالشرح
Abdullahi ɗan mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ambata a cikin faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Duk wanda ya nufe shi da wata fanɗara da zalinci to zamu ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi}. [al-Hajj: 25], ya ce: Da ace wani daga cikin mutane zuciyarsa zata zantar masa cewa ya yi nufin aikata wani mummunan aiki a cikin Haramin Makka wanda zai halatta abinda Allah Ya haramta masa a cikinsa na haram da harshe ne ko kisa da gangan to cewa hakan zalinci ne, kuma da a ce ƙudirin niyyar a birnin Adan ne a cikin (kasar) Yaman to lallai shi mai cancantar Allah Ya azabtar da shi ne da azaba mai raɗaɗi saboda hakan, koda kuwa bai aikata shi ba, niyyar hakan kawai ta ishe shi .فوائد الحديث
Bayanin matsayin da harami ya kebanta da shi da kuma girmama shi .
Al-Sa'adi ya ce: A cikin wannan ayar mai girma, akwai wajabcin ganin alfarmar Harami, da tsananin girmama shi, da gargaɗarwa daga nufin yin saɓo a cikinsa da kuma aikata (saɓon).
Al-Dahhak ya ce: Lallai mutum zai yi niyyar aikata kuskure a Makka alhali shi yana wata ƙasar daban sai arubuta masa (laifin) alhali bai aikata laifin ba.
التصنيفات
Dalilan Saukar Ayoyi