Ku sanya farare daga tufafinku, domin cewa sune mafi alherin tufafinku, kuma ku yi wa mamatanku likkafani a cikinsu

Ku sanya farare daga tufafinku, domin cewa sune mafi alherin tufafinku, kuma ku yi wa mamatanku likkafani a cikinsu

Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku sanya farare daga tufafinku, domin cewa sune mafi alherin tufafinku, kuma ku yi wa mamatanku likkafani a cikinsu".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana shiryar da maza cewa su sa tafafi masu farin launi da kuma yi wa mamata likkafani a cikinsu; domin cewa sune mafi alherin tufafi.

فوائد الحديث

An so sanya farin tufafi, kuma waninsa na wata kalar ma yana halatta.

An so yi wa mamata likkafani da fararen (tufafi).

Shaukani ya ce: Hadisin yana nuni akan halaccin sanya fari da yi wa mamata likkafani da shi; kasancewarsa ya fi waninsa tsarkaka, amma kasancewarsa ya fi tsarki to wannan zahiri ne, amma kasancewarsa ya fi tsafta domin cewa mafi ƙanƙatar abu idan ya faɗa kansa zai bayyana sai ya fifita.

التصنيفات

Ladaban Tufafi