إعدادات العرض
Duk abinda mai yawansa yake sa maye to kaɗan ɗinsa haramun ne
Duk abinda mai yawansa yake sa maye to kaɗan ɗinsa haramun ne
Daga Jabir ɗan Abbdullahi - Allah Ya ƙara yarda a gare su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk abinda mai yawansa yake sa maye to kaɗan ɗinsa haramun ne".
[Hasan ne] [Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi]
الترجمة
العربية Tiếng Việt Indonesia Nederlands Kiswahili English অসমীয়া ગુજરાતી සිංහල Magyar ქართული Română ไทย Português తెలుగు मराठी ភាសាខ្មែរ دری አማርኛ বাংলা Kurdî Македонски Tagalog Українська ਪੰਜਾਬੀ മലയാളം Moore ಕನ್ನಡ Türkçe پښتو Bosanski हिन्दीالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa dukkan abin sha ko abin ci da yake kawar da hankali lokacin da aka ci ko aka sha mai yawa daga gare shi, to cin kaɗan daga gare shi abin haramtawa ne koda bai tafiyar da hankali ba.فوائد الحديث
Kiyayewar shari'a akan hankulan mutane.
Ingancin lura da toshe kafa, hakan ta hanyar kulle dukkan abinda yake kaiwa zuwa waɗannan munanan abubuwan.
Haramta kaɗan na abinda yake sa maye; domin shi tsani ne ga maye.
idan kaɗan ɗinsa ko mai yawansa baisa maye ba, to shi ba haramun ba ne.
التصنيفات
Abubuwan Shan da aka Haramta