Wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba mumini ba ne», aka ce: Waye ya Manzon Allah? ya ce: «Wanda maƙocinsa ba ya aminta daga sharrinsa

Wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba mumini ba ne», aka ce: Waye ya Manzon Allah? ya ce: «Wanda maƙocinsa ba ya aminta daga sharrinsa

Daga Abu Shuraih - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba mumini ba ne», aka ce: Waye ya Manzon Allah? ya ce: «Wanda maƙocinsa ba ya aminta daga sharrinsa».

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa kuma ya ƙarfafi rantsuwarsa sau uku, sai ya ce: Wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, sai sahabbai suka tambaye shi : Waye wanda ba mumini ba ya Manzon Allah? ya ce: Wanda maƙocinsa yake jin tsoron yaudararsa da zalincinsa da kuma sharrinsa.

فوائد الحديث

Kore imani ga wanda maƙocinsa ba ya aminta daga zalincinsa da sharrinsa yana nuni akan cewa shi yana daga manyan zunubai, kuma cewa mai aikata shi mai tauyayyen imani ne.

Kwaɗaitarwa mai ƙarfi akan kyautatawa maƙoci da barin cutar da shi da magana ne ko da aiki.

التصنيفات

Sulhu da Hukunce Hukuncen Maqwabtaka