Lallai za'a samu wasu fitintinu, ku saurara sannan a samu wasu fitintinu wanda ke zaune a cikinsu ya fi wanda ke tafiya a cikinsu, mai tafiya ya fi wanda ke gaggawa zuwa garesu,

Lallai za'a samu wasu fitintinu, ku saurara sannan a samu wasu fitintinu wanda ke zaune a cikinsu ya fi wanda ke tafiya a cikinsu, mai tafiya ya fi wanda ke gaggawa zuwa garesu,

Daga Usman al-Shahhaam, ya ce: Ni da Farƙad al-Sabakhi mun tafi zuwa wurin Muslim ɗan Abu Bakrata alhali yana ƙasarsa, sai muka je wurinsa sai muka ce: Shin ka ji babanka yana zantarwa da wani hadisi a game da fitintinu? ya ce: Eh, na ji Abu Bakrata - Allah Ya yarda da shi - yana zantarwa, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai za'a samu wasu fitintinu, ku saurara sannan a samu wasu fitintinu wanda ke zaune a cikinsu ya fi wanda ke tafiya a cikinsu, mai tafiya ya fi wanda ke gaggawa zuwa garesu, ku saurara idan suka sauka ko suka faru wanda yake da raƙuma to ya riski raƙumansa, wanda yake da tumakai to ya riski tumakansa, wanda yake da wata ƙasa to ya risku da ƙasarsa», ya ce sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah to kana ganin wanda ba shi da raƙuma ko tumakai ko ƙasa fa? ya ce: «Ɗayanku ya nufi takobinsa sai ya caka tsinin takobin a dutse, sannan ya tsira idan zai iya tsira, ya Allah shin na isar? ya Allah shin na isar?». Ya ce: sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah shin kana ganin idan aka tilastani har aka tafi da ni zuwa daya daga jama'a biyun, ko daya daga bangarori biyun, sai wani mutum ya dakeni da takobinsa, ko wata kibiya ta zo sai ta kasheni? ya ce: "Zai koma da zunubinsa da kuma zunubinka, kuma ya zama daga 'yan wuta".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Usman al-Shahham da Farƙad al-Sabakhi sun tambayi Muslim ɗan babban sahabi Abu Bakrata - Allah Ya yarda da shi -: Shin ya ji wani hadisi daga babansa daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da fitintinu da yaƙin da zai afku tsakanin musulmai? sai ya ce: Eh, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa za'a samu wasu fitintinu bayan mutuwarsa, kuma waɗannan fitintinun wanda ke zaune babu ruwansa da su ya fi wanda ke tafiya a cikinsu alhali shi ba ya nemansu, yana bincike game da su, mai tafiya a cikinsu ya fi mai gaggawa zuwa garesu yana ta bincike game da su kuma yana tarayya a cikinsu. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da wanda fitina ta sauka ko ta faru a cikin zamaninsa kuma a wurinsa in ya samu wata mafakar da zai fake gare ta; wanda yake da raƙuman da yake kiwo to ya riski raƙumansa, wanda yake da tumakan da yake kiwo to ya riski tumakansa, wanda yake da wata ƙasa da gona to ya risku da ƙasarsa. Sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah shin kana ganin wanda ba shi da makoma fa na raƙuma ko tumakai ko ƙasa? Ya ce: Ya nufi makaminsa sai ya dandaƙa shi ya kamata shi, sannan ya gudu ya tsiratar da kansa da 'ya'yansa idan ya samu ikon tsira. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya shaidar sau uku sai ya ce: Ya Allah shin na isar? ya Allah shin na isar? ya Allah shin na isar? Sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah shin kana ganin idan an tilastani in yi tarayya tare da ɗaya daga sahu biyun, ko ɗaya daga cikin jama'a biyun, sai wani mutum ya dakeni da takobinsa, ko wata kibiya ta zo ta kasheni fa? Ya ce: Zai koma da zunubin kansa da kuma zunubin wanda ya yi kisan, kuma ranar lahira ya zama daga 'yan wuta.

فوائد الحديث

Bada labarin faruwar fitintinu dan gargaɗarwa daga gareta, kuma mutane su yi musu tanadi, kada su kutsa cikinsu, kuma su roƙi Allah haƙuri da tsira daga sharrikansu.

Nawawi ya ce; Faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (Wanda ke a zaune ya fi wanda ke tsaye), har zuwa ƙarshensa, to ma'anarsa bayanin girman haɗarinsu, da kwaɗaitarwa akan nisantarsu, da guje musu, kuma cewa sharrinsu da fitinarsu zai zama akan gwargwadan rataya da su.

Nawawi ya ce: An ɗauke zunubi ga wanda aka tilastawa akan halartar wurin, amma kisa ba'a halatta shi da tilastawa, kai wanda ya tilasta ɗin zai yi laifi akan wanda aka umarta da shi da ijma'in malamai.

Ibnu Hajar ya ce: Wasu sun ce ; Idan wata ƙungiya ta yi wa shugaba tawaye sai ta hanu daga wajibin da ke kanta ta kuma kafa yaƙi to ya wajaba a yaƙeta, haka nan da ƙungiyoyi biyu zasu yi yaƙi to ya wajaba akan kowane mai iko ya riƙe hannun mai kuskuren da kuma taimakon wanda ke kan gaskiya, wannan ita ce maganar jumhur, wasu kuma suka rarrabe bayani, sai suka ce;

Dukkan yaƙin da ya faru tsakanin ƙungiyoyi biyu daga musulmai inda babu wani shugaba ga jama'a to yaƙi a lokacin an hana, sai a saukar da hadisan da ke cikin wannan babin da waninsa akan haka.

Nawawi ya ce: Haƙiƙa malamai sun yi saɓani a yaƙi lokacin fitina, sai wasu suka ce: Ba zai yi yaƙi ba a lokacin fitintinu tsakanin musulmai koda sun shiga gidansa, kuma sun nemi kashe shi, to ba ya halatta ya kare kansa; domin mai neman mai tawili ne, wannan ita ce mazahabar Abu Bakrata sahabi - Allah Ya yarda da shi - da waninsa, Ibnu Umar da Imran ɗan Hussain - Allah Ya yarda da su - da wasunsu suka ce: Ba zai shiga cikinta ba, sai dai idan ya yi nufin kare kansa, to waɗannan mazahabobi biyun sun haɗu akan barin shiga a dukkanin fitintinun Musulunci, mafi yawancin sahabbai da tabi'ai da gamewar maluman Musulunci suka ce: Ya wajaba a taimaki mai gaskiya a lokacin fitintinu, da tsayuwa tare da shi dan kashe 'yan tawaye kamar yadda Madaukakin sarki Ya ce: {To ku kashe wacce ta yi zalincin har sai ta koma zuwa umarnin Allah...} karanta ayar har karshenta, wannan shi ne ingantacce, kuma sun fassara hadisan akan wanda gaskiya ba ta bayyana gare shi ba, ko akan kungiyoyi biyun masu zalinci babu tawili ga wata daga cikinsu.

التصنيفات

Yi wa Shugaba Tawaye