Lallai mumini yana da wata shema a cikin aljanna ta lu'ulu'u ɗaya mai ƙofa a cikinta, tsawonta mil sittin ne, mumini yana da mata a cikinta, mumini zai kewayesu amma sashinsu ba zai ga sashi ba

Lallai mumini yana da wata shema a cikin aljanna ta lu'ulu'u ɗaya mai ƙofa a cikinta, tsawonta mil sittin ne, mumini yana da mata a cikinta, mumini zai kewayesu amma sashinsu ba zai ga sashi ba

Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai mumini yana da wata shema a cikin aljanna ta lu'ulu'u ɗaya mai ƙofa a cikinta, tsawonta mil sittin ne, mumini yana da mata a cikinta, mumini zai kewayesu amma sashinsu ba zai ga sashi ba".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da sashin ni'imar aljanna, kuma lallai cewa mumini a cikin aljanna yana da wata shema mai girma mai yalwar ciki, ta gwal ɗaya wacce a cikinta akwai ƙofa, faɗinta da tsawonta a cikin sama mil sittin ne, a cikin kowane ɓangare da nahiya da kusurwarta daga cikin kusurwoyin ta huɗu akwai mata, sashinsu ba ya ganin sashi, mumini zai kewayesu.

فوائد الحديث

Bayanin girman ni'imar 'yan aljanna.

Kwaɗaitarwa a kan aiki na gari ta hantar bayanin abinda Allah Ya tanadar musu na ni'ima.

التصنيفات

Sifar Al-janna da Wuta