Tarihin Masu kira da Ayyukansu

Tarihin Masu kira da Ayyukansu

1- "Akwai wani sarki a cikin waɗanda ke gabaninku, kuma ya kasance yana da wani matsafi*, lokacin da ya girma, sai ya cewa sarkin: Haƙiƙa ni na girma, ka aiko min da wani yaron da zan koya masa tsafi, sai ya aika masa da wani yaron da zai koya masa, ya kasance akan hanyarsa idan ya shiga akwai mai ibada sai ya zauna a wurinsa ya ji zancensa, sai ya ƙayatar da shi, ya kasance idan zai zo wajen matsafin sai ya wuce ta wajen mai ibadar ya zauna a wurinsa, idan ya zo wajen matsafin sai ya dake shi, sai ya kai ƙarar hakan wajen mai ibadar, sai ya ce: Idan ka ji tsoron matsafin, to ka ce : Iyalaina ne suka tsareni, idan kuma ka ji tsoron iyalanka to ka ce: Matsafi ne ya tsareni. Yana cikin haka sai ga shi ya zo wajen wata babbar dabbar da ta tsare mutane, sai ya ce: A yau ne zan san cewa matsafi ne ya fi ko mai ibada ne ya fi ? sai ya ɗauki wani dutse, sai ya ce: Ya Allah idan al'amarin mai ibadar ne shi ne mafi soyuwa gareKa to Ka kashe wannan dabbar, har mutane su tafi, sai ya jefeta sai ya kasheta, mutane suka wuce, sai ya zo wajen mai ibadar sai ya ba shi labari, sai mai ibadar ya ce masa: Ya kai ɗana kai a yau ka fini, haƙiƙa al'amarinka ya kai abinda ka gani, lallai cewa kai za'a jarrabeka, idan an jarrabeka to kada ka nuna ni, yaron ya kasance yana warkar da makaho da kuturu, kuma yana bawa mutane maganin sauran cututtuka, sai wani ɗan majalisar sarki wanda ya makance ya ji, sai ya zo masa da kyaututtuka masu yawa, sai ya ce: Abinda ke nan saboda kaine na tarasu, idan ka warkar da ni, sai ya ce: Ni bana warkar da wani, kawai Allah ne Yake warkarwa, idan ka yi imani da Allah zan roƙi Allah sai Ya warkar da kai, sai ya yi imani da Allah sai Allah Ya warkar da shi, sai ya zo wajen sarkin, sai ya zauna a wurinsa kamar yadda ya kasance yana zama, sai sarkin ya ce da shi: Waye ya dawo maka da ganinka? Ya ce: Ubangijina, ya ce: Shin kana da wani Ubangijin wanina? ya ce: Ubangijina kuma Ubangijinka Shi ne Allah, sai ya kama shi bai gushe ba yana ta azabtar da shi har saida ya nuna yaron, sai aka zo da yaron, sai sarkin ya ce masa: Yakai ɗana, haƙiƙa tsafinka ya kai har kana iya warkar da makaho da kuturu kana yin kaza da kaza?! sai ya ce: Ni bana warkar da wani, kawai Allah ne Yake warkarwa, sai ya kama shi bai gusheba yana azabtar da shi har sai da ya nuna mai ibadar, sai aka zo da mai ibadar sai aka ce masa: Ka bar Addinika, sai ya ƙi, sai ya sa aka kawo masa zarto sai ya ɗora zartan a tsakiyar kansa, sai ya tsaga shi har saida ɓarikan jikinsa biyu suka faɗi, sannan aka zo da ɗan majalisar sarki sai aka ce da shi: Ka bar Addininka, sai ya ƙi, sai aka ɗora zarton akan tsakiyar kansa, sai ya tsaga shi da shi har sai da ɓangarorin jnikinsa biyu suka faɗi, sannan aka zo da yaron sai aka ce da shi: Ka bar Addininka, sai ya ƙi, sai ya miƙa shi wurin wasu jama'a daga mutanensa, sai ya ce: Ku tafi da shi zuwa dutsen kaza da kaza, ku hau dutsen da shi, idan kun kai ƙololuwarsa idan ya bar Addininsa to (ku kyale shi) inba haka ba fa to ku jeho shi, sai suka tafi da shi zuwa dutsen kaza da kaza sai suka hau dutsen da shi, sai ya ce: Ya Allah ka isar mini su da abinda Ka so, sai dutsen ya girgiza da su sai suka faɗo, sai ya zo yana tafiya zuwa wurin sarkin, sai sarkin ya ce da shi: Me mutanenka suka yi? sai ya ce: Allah Ya isar mini su, sai ya ƙara bada shi ga wasu daga cikin mutanensa sai ya ce: Ku tafi da shi ku ɗauke shi a cikin jirgin ruwa, kuje tsakiyar kogi da shi, idan ya bar Addininsa to inba haka ba fa to ku jefa shi, sai suka tafi da shi, sai ya ce: Ya Allah ka isar mini su da abinda Ka so, sai jirgin ruwan ya kife da su sai suka dilmiye, sai ya zo yana tafiya wurin sarkin, sai sarkin ya ce da shi: Me mutanenka suka yi? sai ya ce: Allah Ya isar mini su, sai ya cewa sarkin: Kai ba zaka iya kasheni ba har sai ka aikata abinda zan umarceka da shi, ya ce: Menene shi? ya ce: Ka tara mutane wuri ɗaya ka tsireni akan wani kututture, sannan ka ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyina, sannan ka sanya mashin a tsakiyar gwafa sannan ka ce: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ka harbeni, lallai kai idan ka aikata hakan to zaka kasheni, sai ya tara mutane a wuri ɗaya, sai ya tsire shi akan wani kututture, sannan ya ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyinsa sannan ya sanya mashin a cikin tsakiyar gwafa, sannan yace: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ya harbe shi sai ya faɗi ta kayakayinsa, sai ya ɗora hannunsa akan kayakayinsa sai ya mutu, sai mutane suka ce: Mun yi imani da Ubangijin yaro, sai aka zo wa sarkin sai aka ce da shi: Shin kana ganin abinda tsoro, haƙiƙa wallahi tsoronka ya faru, mutane sun yi imani, sai ya yi umarni da haƙa rami ta farkon layuka sai aka haƙa kuma aka hura wuta a cikinsu kuma ya ce: Duk wanda bai bar Addininsa ba to ku cusa shi a cikinta, ko a ce masa: Ka faɗa sai suka aikata, har sai da wata mace ta zo alhali a tare da ita akwai wani ɗanta ƙarami, sai ta tsaya taƙi kutsawa ciki, sai ɗan nata ya ce mata: Ya babata ki yi haƙuri lallai cewa ke akan gaskiya kike".