Akwai wani sarki a cikin waɗanda ke gabaninku, kuma ya kasance yana da wani matsafi

Akwai wani sarki a cikin waɗanda ke gabaninku, kuma ya kasance yana da wani matsafi

Daga Suhaib - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Akwai wani sarki a cikin waɗanda ke gabaninku, kuma ya kasance yana da wani matsafi, lokacin da ya girma, sai yacewa sarkin: Haƙiƙa ni na girma, ka aiko min da wani yaron da zan koya masa tsafi, sai ya aika masa da wani yaron da zai koya masa, ya kasance akan hanyarsa idan ya shiga akwai mai ibada sai ya zauna a wurinsa yaji zancensa, sai ya ƙayatar da shi, ya kasance idan zaizo wajen matsafin sai ya wuce ta wajen mai ibadar ya zauna a wurinsa, idan yazo wajen matsafin sai ya dakeshi, sai yakai ƙarar hakan wajen mai ibadar, sai yace: Idan kaji tsoron matsafin, to kace: Iyalaina ne suka tsareni, idan kuma kaji tsoron iyalanka to kace: Matsafi ne ya tsareni, yana cikin haka sai ga shi yazo wajen wata babbar dabbar da ta tsare mutane, sai yace: A yau ne zansan cewa matsafi ne yafi ko mai ibada ne yafi? sai ya ɗauki wani dutse, sai yace: Ya Allah idan al'amarin mai ibadar ne shine mafi soyuwa gareKa to Ka kashe wannan dabbar, har mutane su tafi, sai ya jefeta sai ya kasheta, mutane suka wuce, sai yazo wajen mai ibadar sai ya bashi labari, sai mai ibadar yace masa: Ya kai ɗana kai a yau ka fini, haƙiƙa al'amarinka yakai abinda ka gani, lallai cewa kai za'a jarrabeka, idan an jarrabeka to kada ka nunani, yaron ya kasance yana warkar da makaho da kuturu, kuma yana bawa mutane maganin sauran cututtuka, sai wani ɗan majalisar sarki wanda ya makance yaji, sai yazo masa da kyaututtuka masu yawa, sai yace: Abinda ke nan saboda kaine na tarasu, idan ka warkar da ni, sai yace: Ni bana warkar da wani kawai Allah ne Yake warkarwa, idan kayi imani da Allah zan roƙi Allah sai Ya warkar da kai, sai yayi imani da Allah sai Allah Ya warkar da shi, sai yazo wajen sarkin, sai ya zauna a wurinsa kamar yanda ya kasance yana zama, sai sarkin yace da shi: Waye ya dawo maka da ganinka? Ya ce: Ubangijina, yace: Shin kana da wani Ubangijin wanina? yace: Ubangijina kuma Ubangijinka Shine Allah, sai ya kamashi bai gushe ba yana ta azabtar da shi har sai da ya nuna yaron, sai akazo da yaron, sai sarkin yace masa: Yakai ɗana, haƙiƙa tsafinka yakai har kana iya warkar da makaho da kuturu kana yin kaza da kaza?! sai yace: Ni bana warkar da wani, kawai Allah ne Yake warkarwa, sai ya kamashi bai gusheba yana azabtar da shi har sai da ya nuna mai ibadar, sai akazo da mai ibadar sai akace masa: Kabar Addinika, sai yaƙi, sai yasa aka kawo masa zarto sai ya ɗora zartan a mararrabar kansa, sai ya tsagashi har sai da ɓarikan jikinsa biyu suka faɗi, sannan akazo da ɗan majalisar sarki sai akace da shi: Kabar Addininka, sai yaƙi, sai aka ɗora zarton akan mararrabar kansa, sai ya tsagashi da shi har sai da ɓangarorin jnikinsa biyu suka faɗi, sannan akazo da yaron sai akace da shi: Kabar Addininka, sai yaƙi, sai ya miƙashi wurin wasu jama'a daga mutanensa, sai yace: Ku tafi da shi zuwa dutsen kaza da kaza kuhau dutsen da shi, idan kun kai ƙololuwarsa idan yabar Addininsa to inba haka bafa to ku jehoshi, sai suka tafi da shi zuwa dutsen kaza da kaza sai suka hau dutsen da shi, sai yace: Ya Allah ka isar mini su da abinda Ka so, sai dutsen ya girgiza da su sai suka faɗo, sai yazo yana tafiya zuwa wurin sarkin, sai sarkin yace da shi: Me mutanenka suka yi? sai yace: Allah Ya isar mini su, sai ya ƙara bada shi ga wasu daga cikin mutanensa sai yace: Ku tafi da shi ku ɗaukeshi a cikin jirgin ruwa, kuje tsakiyar kogi da shi, idan yabar Addininsa to inba haka bafa to ku jefashi, sai suka tafi da shi, sai yace: Ya Allah ka isar mini su da abinda Ka so, sai jirgin ruwan ya kife da su sai suka dilmiya, sai yazo yana tafiya wurin sarkin, sai sarkin yace da shi: Me mutanenka sukayi? sai yace: Allah Ya isar mini su, sai yacewa sarkin: Kai bazaka iya kasheni ba har sai ka aikata abinda zan umarceka da shi, yace: Menene shi? yace: Ka tara mutane abigire ɗaya ka tsireni akan wani kututture, sannan ka ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyina, sannan ka sanya mashin a tsakiyar gwafa sannan kace: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ka harbeni, lallai cewa kai idan ka aikata hakan to zaka kasheni, sai ya tara mutane a bigire ɗaya, sai ya tsireshi akan wani kututture, sannan ya ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyinsa sannan ya sanya mashin a cikin tsakiyar gwafa, sannan yace: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ya harbeshi sai ya faɗi ta kayakayinsa, sai ya ɗora hannunsa akan kayakayinsa sai ya mutu, sai mutane suka ce: Munyi imani da Ubangijin yaro, sai akazowa sarkin sai akace da shi: Shin kana ganin abinda tsoro haƙiƙa wallahi tsoronka ya faru, mutane sunyi imani, sai yayi umarni da haƙa rami ta farkon layuka sai aka haƙa kuma aka hura wuta a cikinsu kuma yace: Duk wanda bai bar Addininsa ba to ku cusa shi a cikinta, ko ace masa: Ka faɗa sai suka aikata har sai da wata mace tazo alhali a tare da ita akwai wani ɗanta ƙarami, sai ta tsaya taƙi kutsawa ciki, sai ɗan nata yace mata: Ya babata kiyi haƙuri lallai cewa ke akan gaskiya kike".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai wani sarki cikin waɗanda ke gabanmu daga cikin al'ummatai, ya kasance yana da wani matsafi, lokacin da matsafin ya girma, sai yacewa sarkin: Lallai ni na girma, to ka aika wani saurayi zuwa gurin in koya masa tsafi. Sai sarkin ya aika masa da wani saurayin da zai koya masa, a kan hanyar saurayin idan zai tafi gurin matsafin akwai wani mai ibada sai ya zauna a wurinsa sau ɗaya yaji zancensa, sai ya ƙayatar da shi, ya kasance idan yazo wurin matsafin sai yawuce wurin mai ibadar ya zauna a wurinsa, idan kuma yaje wurin matsafin sai ya dakeshi saboda jinkirin da yayi, sai yakai ƙarar hakan wurin mai ibadar, sai yace: Idan kaji tsoron matsafin, to kace: Iyalaina ne suka tsareni, idan kuma kaji tsoron iyalanka to kace: Matsafi ne ya tsareni, sun kasance a haka lokacin da yazowa wata babbar dabba ta hana mutane wucewa, sai yace: A yau ne zan san cewa matsafi ne yafi ko kuma mai ibada ne yafi? Sai ya ɗauki wani dutse, sai yace: Ya Allah idan al'amarin wannan mai ibadar ne mafi soyuwa gareKa daga al'amarin matsafin nan to Ka kashe wannan dabbar, har mutane su wuce, sai ya jefeta sai ya kasheta, kuma mutane suka wuce, sai yazo wajen mai ibadar sai ya bashi labari, sai mai ibadar yace masa: Yakai ɗana kai a yau ka fini, haƙiƙa al'amarinka ya kai abinda kake gani, kuma lallai za'a jarrabeka, idan an jarrabeka to kada ka nuna ni, yaron ya kasance yana warkar da makaho da kuturu, yana bawa mutane maganin sauran cututtuka da izinin Allah, sai wani ɗan majalisar sarki wanda ya rasa ganinsa ya ji, sai yazo masa da kyautuka masu yawa, sai yacewa yaron: Dukkan abinda ke nan na kyautuka naka ne idan ka warkar da ni. Sai yace: Lallai cewa ni bana warkar da wani kawai Allah ne Yake warkarwa, idan kayi imani da Allah zan roƙi Allah Ya warkar da kai, sai yayi imani da Allah sai Allah Ya warkar da shi, sai yazo wajen sarkin sai ya zauna a wurinsa kamar yanda ya kasance yake zama, sai sarkin yace masa: Waye ya mayar maka da ganinka? Yace: Ubangijina, yace: Shin kana da wani Ubangijin wanina? Yace: Ubangijina da Ubangijinka shine Allah. Sai ya kamashi bai gushe ba yana azabtar da shi har sai da ya nuna yaron, sai akazo da yaron, sai sarkin yace masa: Yakai ɗana haƙiƙa tsafinka yakai har kana warkar da makaho da kuturu, kana aikata kaza da kaza. Sai yace: Ni bana warkar da wani, kawai Allah ne Yake warkarwa, sai ya kamashi bai gushe ba yana azabtar da shi har sai da ya nuna mai ibadar. Sai akazo da mai ibadar, sai akace da shi: Kabar Addininka, sai yaƙi, sai yace akawo masa zarto, sai ya ɗorashi akan mararrabar kansa, sai ya raba shi gida biyu. Sannan akazo da ɗan majalisar sarkin sai akace da shi: Kabar Addininka, sai ya ƙi sai ya sanya zarto akan mararrabar kansa, sai ya rabashi gida biyu. Sannan akazo da yaron sai akace masa kabar Addinika, sai ya ƙi sai ya miƙashi gurin wasu mazaje daga mutanensa tsakanin uku da goma. Sai yace: Ku tafi da shi zuwa dutsen kaza da kaza, kuhau dutsen da shi, idan kun kai ƙololuwarsa, idan ya bar Addininsa to, inba haka bafa to ku jehoshi, sai suka tafi da shi sai suka hau dutsen da shi. Sai yaron yace: Ya Allah ka isar mini su da abinda Ka so, sai dutsen ya girgiza da su yayi motsi motsi mai tsanani sai suka faɗo, sai yazo yana tafiya zuwa gurin sarkin. Sai sarkin yace masa: Me mutanenka suka yi? Yace: Allah Ya isar mini su. Sai ya miƙashi zuwa wasu mutane daga cikin mutanensa, sai yace: Ku tafi da shi ku ɗaukeshi a cikin ƙaramin jirgin ruwa, sai ku tafi tsakiyar kogi da shi, idan ya bar Addininsa inba haka bafa to ku jefashi a cikin kogin. Sai suka tafi da shi, sai yace: Ya Allah Ka isar mini su da abinda Ka so, sai jirgin ruwan ya kife da su sai suka dilmiya, sai yazo yana tafiya wurin sarkin. Sai sarkin yace masa: Me mutanenka sukayi? Sai yace: Allah Ya isar mini su, sai yaron yacewa sarkin: Lallai cewa kai bazaka iya kasheni ba har sai ka aikata abinda zan umarceka da shi. Yace: Menene shi? Yace: Ka tara mutane a mabayyaniyar ƙasa, ka tsireni akan kututturen bishiya, sannan ka ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyina, sannan ka sanya mashin a tsakiyar kwari, sannan kace: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ka harbeni, lallai cewa kai idan ka aikata haka zaka kasheni, sai ya tara mutane a wuri ɗaya, ya tsireshi akan wani kututture, sannan ya ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyinsa, sannan ya sanya mashin a tsakiyar kwari, sannan yace: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ya harbeshi sai mashin ya faɗa a kayakayinsa tsakanin idanuwansa da kunnansa, sai ya ɗora hannunsa a kayakayinsa a wurin da mashin (ya faɗa) sai ya mutu. Sai mutane sukace: Munyi imani da Ubangijin yaro, munyi imani da Ubangijin yaro, munyi imani da Ubangijin yaro. Sai akazowa sarkin akace masa: Shin kaga abinda ka kasance kana jin tsoro? Haƙiƙa wallahi abinda kaji tsoro ya sauka shine mutane suna bin yaron da yin imani da Ubangijin yaron bakiɗayansu, sai yayi umarni a tsaga ƙasa ayi manyan ramuka masu tsawo a ƙofofin hanyoyi, aka kunna wuta a cikinsu, kuma yace: Duk wanda bai bar Addininsa ba to ku jefashi a cikinta, sai suka aikata abinda sarkin ya umarcesu da shi, har wata mace tazo atare da ita akwai wani ɗanta ƙarami, sai ta tsaya ta lazimci inda take taƙi shiga cikin wutar, sai ɗanta yace mata: Ya babata kiyi haƙuri, lallai ke akan gaskiya kike.

فوائد الحديث

Tabbatar da karamomin waliyyai, daga hakan akwai kashe babbar dabba ta hanyar jifan yaron, da kuma amsa addu'ar yaron sau biyu, da kuma maganar ƙaramin yaron da ake shayar da shi.

Taimakon wanda ya dogara ga Allah - tsarki ya tabbatar maSa -.

Bayanin ɗaukakar haƙuri da kuma tabbata akan Addini.

Hikima a cikin neman ilimi a farkon rayuwa; domin cewa saurayi a galibi yafi saurin hadda daga babba.

Ƙarfin imanin wannan yaron, kuma cewa baiyi nisa da imaninsa ba bai kuma juya baya ba.

Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yana amsa kiran wanda ke cikin tsananin buƙata idan ya kiraShi.

Mutum yana halatta ya ruɗar da kansa a cikin maslahar dukkanin musulmai, domin cewa wannan yaron ya nunawa sarki abinda zai kasheshi da shi ya kuma halakar da kansa da shi, shine ya ɗauki mashi daga cikin kibiyoyinsa ya sanya shi a tsakiyar kwari sai yace: Da sunan Allah Ubangijin yaro.

Halaccin yin ƙarya a cikin yaƙi da makamancinsa, da kuma tsamo rai daga halaka.

Mumini ana jarrabarsa a cikin gaskiyar imaninsa da kuma tabbata akan faɗin gaskiya, ko da al'amarin zai kaishi ga tafiyar da ransa.

Bada rai ta hanyar kira zuwa ga Allah da kuma bayyanar da gaskiya.

Zukatan bayi suna hannun Allah Yana shiryar da wanda Yake so kuma Yana ɓatar da wanda Yake so, haƙiƙa yaron ya shiriya alhali shi yana cikin renon matsafi da kuma kulawar sarki mai laifi.

Halaccin roƙon Allah - Maɗaukakin sarki - Ya nunawa bawa alamar da zai san daidai da ita kuma yaƙini ya tabbata gareshi.

Masu imani suna bada dukkan abinda Allah Ya basu kuma Yayi musu falala da shi dan yiwa Addininsa hidima da kuma kira zuwa ga tarkinSa.

Sabubban halaka suna hannun Allah, idan Ya so sai Ya zartar da su idan kuma ya so sai ya yanke su.

Kafirai hujjoji da dalilai basa tauyesu dan yin imani, kawai sababin kafircinsu shine shisshigi da kuma girman kai.

Ɗagutai da azzalumai akwai suna da tanadi dan kashe mutane bakiɗaya dan su wanzu akan abinda suke a cikinsa na ni'imar duniya.

Allah Yana yiwa azzalumai uƙuba ta inda basa zato, haƙiƙa mutane sunyi imani da Ubangijin yaro lokacin da sukaga tabbatarsa da gaskiyar da'awarsa da kuma rashin tsoronsa ga zargin mai zargi saboda Allah.

Akwai waɗanda sukayi magana suna tsumman goyo banda (Annabi) Isa - aminci ya tabbata agare shi -, wannan hadisin yana bayanin faɗin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Babu waɗanda sukayi magana a cikin shinfiɗar goyo sai mutum uku...", sai ya ambacesu, ya kuma taƙaitasu a cikin Banu Isra'il banda wasunsu.

التصنيفات

Tarihin Masu kira da Ayyukansu, Qissosi da labaran Al-umman da suka gabata