Yaku wannan mata, ku yi sadaka, dan ni an nuna min cewa kune mafi yawan 'yan wuta". Sai suka ce: Dan me ya Manzon Allah? ya ce: "Kuna yawaita tsinuwa, kuma kuna butulcewa zamantakewa, banga masu tawayar hankali da Addini mafi tafiyar da hankalin namiji ba mai karfin niyya kamar ɗayanku ba

Yaku wannan mata, ku yi sadaka, dan ni an nuna min cewa kune mafi yawan 'yan wuta". Sai suka ce: Dan me ya Manzon Allah? ya ce: "Kuna yawaita tsinuwa, kuma kuna butulcewa zamantakewa, banga masu tawayar hankali da Addini mafi tafiyar da hankalin namiji ba mai karfin niyya kamar ɗayanku ba

Daga Abu Sa'ida Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita zuwa wurin da ake sallah, a babbar sallah ko a ƙarama, sai ya wuce inda mata suke, sai ya ce: "Yaku wannan mata, ku yi sadaka, dan ni an nuna min cewa kune mafi yawan 'yan wuta". Sai suka ce: Dan me ya Manzon Allah? ya ce: "Kuna yawaita tsinuwa, kuma kuna butulcewa zamantakewa, banga masu tawayar hankali da Addini mafi tafiyar da hankalin namiji ba mai karfin niyya kamar ɗayanku ba", suka ce: To menene tawayar Addininmu da hankalinmu ya Manzon Allah? ya ce: "Shin yanzu bai zama cewa shaidar mace kwatankwacin rabin shaidar namiji ba ce" suka ce: Eh, ya ce: "To wannan yana daga tawayar hankalinta, shin yanzu idan ta yi al’ada ba ta sallah ba ta azimi" suka ce: Eh, ya ce: "To wannan yana daga tawayar Addininta".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita a ranar idi zuwa wurin sallah, ya kasance haƙiƙa ya yi wa mata alƙawarin cewa zai waresu da wa'azi, sai ya zartar da shi a wannan ranar, kuma ya ce: Yaku wannan jama'a ta mata ku yi sadaka, kuma ku yawaita istigfari; su suna daga mafi girman sabubban kawar da kurakurai, domin cewa ni na ganku a daren Isra'i mafi yawan 'yan wuta. Sai wata mace daga cikinsu mai hankali da tunani da nutsuwa ta ce: Meke damu ya Manzon Allah (mune) mafi yawancin 'yan wuta? Ya ce: Dan wasu al'amuara: Kuna yawaita tsinuwa da zagi, kuma kuna musun haƙƙin miji. Sannan ya siffanta su da faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ban ga masu tawayar hankali da Addini ba mafi rinjaye ga ma'abocin tinani da hankali da karfin niyya da kiyayewa ga al'amari ba kamar ku. Ta ce: Ya Manzon Allah, menene tawayar hankali da Addini? Ya ce: Amma tawayar hankali to shaidar mace biyu ta yi daidai da shaidar namiji ɗaya; to wannan tawayar hankali ne, tawayar Addini ita ce tawayar aiki na gari inda zata zauna wasu darere da kwanuka ba ta sallah saboda al’ada, kuma tana ajiye azimi wasu kwanuka saboda al’ada, to wannan tawayar Addini ne, sai dai cewa su ba'a zarginsu akan hakan kuma ba'a kamasu akan su ; domin cewa shi yana daga asalin halitta, kamar yadda mutum an ɗabi'antar da shi kuma an halicce shi yana son dukiya kuma mai gaggawa a al'amuransa kuma mai jahilci...da wanin haka, sai dai ya faɗakar akan hakan dan gargaɗarwa daga fitinuwa da su.

فوائد الحديث

An so fitar mata zuwa sallar Idi, kuma a waresu da wa'azi.

Butulcewa hakkin miji da yawan tsinuwa yana daga manyan zunubai; domin cewa narko da wuta yana daga alamar kasancewar saɓon babba ne.

A cikinsa akwai bayanin ƙaruwar imani da tawayarsa, wanda bautarsa ta yi yawa sai imaninsa da Addininsa ya ƙaru, wanda ibadarsa ta tawaya to Addininsa ya ragu.

Al-Nawawi ya ce: Hankali yana karɓar ƙari da ragi, haka nan imani, abin nufi da ambatan tawaya a mata bai zama zarginsu akan hakan ba; domin cewa shi yana daga asalin halitta, sai dai faɗakarwa akan hakan gargaɗarwa ne daga fitinuwa da su, saboda haka ne ya jeranta azaba akan abinda aka ambata na butulci da waninsa ba akan tawaya ba, kuma tawayar Addini ba ta zama mai taƙaituwa a cikin abinda zunubi yake faruwa da shi ba a cikin nafi gamewa daga hakan.

A cikinsa akwai tattaunawar mai neman ilimi ga malami da mai bi ga wanda ake bi a cikin abinda idan ma'anarsa ba ta bayyan ba.

A cikinsa cewa shaidar mace tana a kan rabin shaidar namiji to hakan dan ƙarancin kiyayewarta ne.

Ibnu-Hajar ya ce a cikin faɗinsa: "Ban ga daga masu tawayar..." yana bayyana gareni cewa hakan yana cikin jumlar sabubban kasancewarsu mafi yawancin 'yan wuta; domin cewa su idan sun kasance sababi na tafiyar da hankalin namiji mai karfin niyya har ya aikata ko ya faɗi abinda bai kamata ba to haƙiƙa sun yi tarayya da shi a cikin zunubi sun kuma yi ƙari a kansa.

Haramcin sallah da azimi akan mace a lokacin al’adarta, kwatankwacinta mai jinin biƙi, sannan zasu rama azimi kawai a halin tsarkinsu.

Kyakkyawan ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - haƙiƙa ya amsawa mata game da tambayarsu ba tare da tsanantawa ko zargi ba.

Ibnu Hajar ya ce: Cewa sadaka tana tunkuɗe azaba, kuma ita zata iya kankare zunuban dake tsakanin halittu.

Al-Nawawi ya ce: Tawayar Addini a wurin mata saboda barinsu sallah da azimi ne a lokacin al’ada; domin cewa wanda ibadarsa ta yawaita to sai imaninsa da Addininsa su ƙaru, wanda ibadarsa ta tawaya sai Addininsa ya tawaya, sannan tawayar Addini zata iya zama ta fuskar da zai iya samun zunubi, kamar wanda ya bar sallah ko azimi ko waninsu na ibadu na wajibai ba tare da wani uzuri ba, kuma zai iya zama ta fuskar da babu laifi a cikinsa kamar wanda ya bar Juma'a ko yaƙi ko wanin haka daga abinda ba ya wajaba akansa ba tare da wani uzuri ba, kuma zai iya zama ta fuskar da shi an dora masa ne kamar barin mai al’ada sallah da azimi.

التصنيفات

Hukunce Hukuncen Mata, Sifar Al-janna da Wuta