Wanda ya kiyaye akan raka'o'i huɗu kafin azahar da huɗu a bayanta Allah Zai haramta wuta gare shi

Wanda ya kiyaye akan raka'o'i huɗu kafin azahar da huɗu a bayanta Allah Zai haramta wuta gare shi

Daga Ummu Habiba - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Wanda ya kiyaye akan raka'o'i huɗu kafin azahar da huɗu a bayanta Allah Zai haramta wuta gare shi ".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa wanda ya yi sallar nafila raka'a huɗu kafin sallar Azahar, da raka'o'i huɗu a bayanta albishir, kuma ya dawwama ya kiyaye akansu (cewa) Allah Zai haramta wuta gare shi .

فوائد الحديث

An so kiyayewa akan raka'o'i huɗu kafin Azahar da (raka'o'i) huɗu a bayanta.

Salloli ratibai kafin sallah - wato kafin farillah -; suna da hikimomi, daga cikinsu: Yi wa zuciyar mai sallah tanadi ga ibada kafin shiga cikin farilla, amma na bayan sallah daga cikin hikimominsu akwai gyara kuskure a farillai.

Akwai fa'idoji da yawa a (salloli) ratibai, na ƙarin kyawawan ayyuka, da kankare munanan ayyuka, da ɗaga darajoji.

Ka'idojin Ahlus Sunnah a cikin hadisan alkawari irin wannan hadisin: Ita ce a ɗauki (hadisan) akan mutuwa akan tauhidi, kuma cewa abin nufi rashin dawwama a cikin wuta; domin mai aikata zunubai cikin masu tauhidi ya cancanci uƙuba sai dai ba zai dawwama a cikin wuta ba in an yi masa uƙuba.

التصنيفات

Sunnoni Ratibai