إعدادات العرض
Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alokacin yana kan mimbari, me kake gani a kan sallar dare, sai ya ce: «Biyu-biyu ce
Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alokacin yana kan mimbari, me kake gani a kan sallar dare, sai ya ce: «Biyu-biyu ce
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alokacin yana kan mimbari, me kake gani a kan sallar dare, sai ya ce: «Biyu-biyu ce», idan ya ji tsoron (ɓullowar) Asuba sai ya sallaci raka'a ɗaya, sai ta yi masa wutirin abin da ya sallata» kuma shi ya kasance yana cewa «Ku sanya ƙarshen sallarku ta zama witiri» domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da shi.
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو हिन्दी 中文 Tiếng Việt ئۇيغۇرچە Kurdî Português دری Македонски Magyar ქართული ไทย অসমীয়াالشرح
Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tattaba agare shi - a lokacin yana huɗuba akan mimbari: Ya Manzon Allah ka sanar da ni yaya zan yi sallar dare? Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka yi sallah ka sallame daga kowadanne raka’oi biyu, idan ka ji tsoron ɓullowar asuba to ka sallaci raka'a ɗaya sai ta yi maka wutirin abin da ka sallata, kuma cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wasicci da a sanya ƙarshen sallar dare ta zama witiri.فوائد الحديث
Asali a cikin sallar dare shi ne ya yi sallama daga kowadanne raka’oi biyu, banda witiri.
Cewa sallar dare ba'a ƙayyade ta da wani adadi ba; dan wawaitar da lafazin.
Nawawi ya ce: "Sallar dare da rana raka'a biyu-biyu ce", wannan abin ɗauka akan bayanin a bin da ya fi, shi ne ya yi sallama daga kowanne raka’oi biyu, kuma daidai ne nafilfilin dare da na rana an so mai sallah ya yi sallama daga kowanne raka’oi biyu.
Nawawi ya ce: A cikin wannan a kwai dalili akan sunna ita ce a sanya witiri a ƙarshen sallar dare, kuma lokacinsa yana fita ne da zarar alfijir ya ɓullo, shine mafi shahara a mazahabarmu, kuma da shi ne jumhur na malamai suka faɗa.
التصنيفات
Tsayuwar Dare