إعدادات العرض
Sallar jam'i ta fi sallar ɗayanku shi kaɗai, da yanki ashirin da biyar, kuma mala'ikun dare da mala'ikun rana suna taruwa a sallar Asuba
Sallar jam'i ta fi sallar ɗayanku shi kaɗai, da yanki ashirin da biyar, kuma mala'ikun dare da mala'ikun rana suna taruwa a sallar Asuba
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Sallar jam'i ta fi sallar ɗayanku shi kaɗai, da yanki ashirin da biyar, kuma mala'ikun dare da mala'ikun rana suna taruwa a sallar Asuba" Sannan Abu Huraira ya ce: Idan kun so ku karanta: {Lallai karatun alfijir (sallar Asuba) ya kasance abin halartowar (mala'iku) ne} [al-Isra'i: 78].
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو हिन्दी Tagalog 中文 Kurdî Português Tiếng Việt Kiswahili Nederlands অসমীয়া ગુજરાતી සිංහල Magyar ქართული Românăالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa lada da sakamakon sallar mutum a cikin jama'a tare da liman ya fi sallah ashirin da biyar da mutum zai sallace su shi kaɗai a cikin gidansa ko kasuwarsa, sannan (annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa mala'ikun dare da rana suna taruwa a sallar Asuba, sannan Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce yana mai kafa hujja akan hakan: Idan kun so ku karanta: {Lallai karatun alfijir (sallar Asuba) ya kasance abin halartar (mala'iku) ne} [al-Isra'a: 78]. Wato: Lallai sallar Asuba mala'ikun dare da mala'ikun rana suna halartarta.فوائد الحديث
Ibnu Hajar ya ce: Lallai sallah a cikin masallaci a jam'i tana ƙaruwa akan sallah a cikin gida da cikin kasuwa a jam'i da ɗaiɗaiku, Ibnu Daƙiƙul Eid ma ya faɗi hakan.
A cikinsa akwai falalar sallar Asuba; dan keɓantuwar mala'iku da ita.
Ibnu Baaz ya ce: Yana kamata ga mumini ya yi kwaɗayin kiyaye sallah a cikin jama'a koda gidansa ya yi nisa dan ya samu wannan alherin mai girma.
Nawawi ya faɗa a akan haɗa wadannan ruwayoyin cewa sallar jama'a ta fi sallar mutum ɗaya da daraja ashirin da biyar, ɗaya riwayar kuma da ashirin da bakwai: Haɗawa tsakaninsu ta fuskoki uku ne:
Ta farkonsu: Cewa babu korewa (tsakaninsu), ambatan kaɗan ba ya kore mai yawa, kuma mafhumul adadi ɓatacce ne a wurin malaman Usulul Fiƙhi.
Na biyu: Ta zama tun farko ya labarta kaɗan ɗin, sannan Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanar da shi ƙarin falala, sai ya bayar da bayaninta.
Na uku: Cewa shi ya banbanta a tsakanin yanayin masallata da kuma sallar, sai ta zama ashirin da biyar ga wasunsu, ga wasunsu kuma ashirin da bakwai gwargwadan cikar sallar da kuma kiyayewarsa akan siffarta da kushu'inta da yawan jama'arta da falalarsu da kuma darajar wurin (sallar) da makamancin hakan. Allah ne Mafi sani.