Duk wanda ya riki kare, to kullum ana rage masa kiradi biyu daga ladansa, sai dai in na farauta ne ko mai kula da dabbobi

Duk wanda ya riki kare, to kullum ana rage masa kiradi biyu daga ladansa, sai dai in na farauta ne ko mai kula da dabbobi

Daga Abdullahi Dan Umar- Allah ya yarda da su- zuwa ga Annabi: "Duk wanda ya riki kare, to kullum ana rage masa kiradi biyu daga ladansa, sai dai in na farauta ne ko mai kula da dabbobi". Sai Salim yace: Abu Huraira ya kasance yana yana cewa: " ko karen noma" Abu Huraira ya kasace manomi

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Kare na daga cikin kaskantattun kazaman dabbobi, don haka shari'a mai tsarki ta hana a ike shi sabo da gudun cutarwa da barna, kasancewar Mala'iku na yin nesa da gidan da yake da kare, hakanan saboda tsoratarwa da razanarwa da najasa da cutarwa, da kuma wauta . duk wanda ke da kare zaa ke rage wani abu mai girma cikin ladansa, kwatankwacinsa girman kiradi biyu, Allah shi ne mafi sani, saboda yin haka sabon Allah ne. Idan akwai bukatar yin hakan to babu laifi cikin daya daga abubuwa uku: Na daya: Gadin dabbobin da ake jiye musu tsoron kyarkeci da barayi. Na biyu: Gadin dabobi. Na uku: Don yin farauta. Don wadannan amfanunuka za'a iya rikar kare kuma ba wani zargi a kan mutum.

التصنيفات

Farauta