Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni naga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba

Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni naga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba

Daga Umar - Allah ya yarda da shi -: Cewa shi ya zo wurin Hajarul Aswad (Baƙin dutse) sai ya sumbace shi, sai ya ce: Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni naga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Sarkin muminai Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya zo wajen Hajarul Aswad a kusurwar Ka'aba sai ya sunbace shi, sai ya ce: Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni na ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba.

فوائد الحديث

Halaccin sunbatar Hajarul Aswad ga masu ɗawafi lokacin da suka yi daura da shi, idan zai yi wu kuma cikin sauƙi.

Abin nufi daga sunbatar Hajaraul Aswad, shi ne bin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Nawawi ya ce: Ma'anarsa cewa babu wani iko gare shi akan anfanarwa ko cutarwa, kuma cewa shi dutse ne abin halitta kamar ragowar halittun da basa cutarwa kuma basa anfanarwa, kuma (sayyadina) Umar ya yaɗa wannan ne a lokacin Mausim (Hajji); dan ya shaida waa kasashe, kuma ma'abota Mausim (Hajji) mabanbantan ƙasashe su kiyaye.

Ibadu a tsaye suke (ababen shara'antawa ne daga Allah da ManzonSa kadai); ba'a shara'anta wani abu na ibada sai abinda Allah da ManzonSa suka shara'anta.

Idan ibada ta inganta za’a yi aiki da ita koda ba'asan hikimarta ba; domin cewa rikon da mutane suka yi da umarni da kuma biyayyarsu a kan tsayuwa da ita yana daga hikimomi ababen nufi.

Hani daga sunbatar abinda shari'a ba ta zo da sunbatarsa ba ta hanyar bauta na duwatsu da wasunsu.

التصنيفات

Falalar Sahabbai -Amincin Allah a gare su-, Hukunce Hukunce da Ma'alolin Hajji da Umra