إعدادات العرض
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana koya mana Istikhara a cikin al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga Alƙur'ani
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana koya mana Istikhara a cikin al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga Alƙur'ani
Daga Jabir ɗan Abdullah -Allah Ya yarda da su -, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana koya mana Istikhara a cikin al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga Alƙur'ani, yana cewa: «Idan ɗayanku ya yi niyyar yin wani al'amari to ya yi (sallah) raka'a biyu ba ta farilla ba, sannan ya ce: Ya Allah ni ina neman zaɓinKa da saninKa, kuma ina neman ikonKa da ikonKa, ina roƙonKa daga falalarKa mai girma, domin cewa Kai Kana da iko ni ba ni da iko, kuma Kana sani ni kuma bani da sani, kaine Masanin abinda ke ɓoye, ya Allah idan Kasan cewa wannan al'amarin alheri ne a cikin Addinina, da rayuwata da ƙarshen al'amarina» ko cewa ya yi: "Magaggaucin al'amarina da kuma majirkincinsa, to ka kaddara mini shi kuma ka sawwaka mini shi sannan Ka yi albarka gareni a cikinsa, idan kuma Kasan cewa wannan al'amarin sharri ne gareni a cikin Addinina da rayuwata da karshemn al'amarina" ko cewa ya yi: "A cikin magaggaucin al'amarina da majirkincinsa, to ka kawar da shi daga gareni ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara mini alheri a duk inda yake, sannan Ka yarda da ni" Ya ce: "Sai ya ambaci buƙatarsa».
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Bahasa Indonesia Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Français ئۇيغۇرچە Kurdî Русский Tiếng Việt অসমীয়া Nederlands Kiswahili አማርኛ සිංහල ไทยالشرح
Idan musulmi ya yi nufin aikata wani al'amari daga abinda bai san ina ne daidai a cikinsa ba, to an shara'anta masa ya yi sallar Istikhara yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana koyawa sahabbansa - Allah Ya yarda da su - wannan sallar kamar yadda yake koya musu sura daga Alƙur'ani, sai ya yi sallah raka'a biyu ba ta farilla ba, sannan ya roƙi Allah yana mai cewa: «Ya Allah ni ina neman zaɓinKa» da neman dacewa da zaɓin al'amura biyu, kuma ina roƙonKa «da saninKa» mayalwaci wanda ya kewaye kowane abu, «ina neman ikonKa» Ka sanya ni mai iko inda babu wata dabara gareni kuma babu wani ƙarfi sai naKa «Da ikonKa» mai zarcewa Kai wani abu ba ya gajiyar da Kai, «Ina roƙonKa daga falalarKa» da kyautatawarKa «mai girma» mayalwaciya; yadda kyautarKa falala ce daga gareKa, kuma babu wani haƙƙi a cikin ni'ima ga wani a kanKa; «domin cewa Kai Kana da iko» akan dukkan komai, ni kuma mai rauni ne gajiyayye «bani da iko» akan wani abu sai da taimako daga gareKa, «Kai» "kana sani" da saninKa mai tattarowa mai kewayewa da zahiri da kuma badini, da alheri da kuma sharri, "ni" "bana sani" wani abu sai da dacewarKa da kuma shiryarwarKa, "Kai ne Masanin abinda ke boye" ilimi kai tsaye naKa ne, da iko mai zarcewa, babu haka ga waninKa sai dai abinda ka kaddara masa da kuma abinda Ka ba shi iko akansa. Sannan musulmi ya roƙi Ubangijinsa, ya ambaci buƙatarsa sai ya ce: «Ya Allah» ni na fawwala al'amarina gareKa «idan Kasan cewa» a cikin saninKa cewa wannan al'amarin «sai ya ambaci buƙatarsa» kamar siyan wannan gidan, ko a cikin siyan wannan motar, ko a cikin auren wannan matar mo wanin hakan... Idan wannan al'amarin ya kasance ya rigaya a cikin saninKa cewa a cikinsa «alheri ne a cikin Addini na» wanda shi ne igiyar al'amarina, «da rayuwata» a cikin duniyata «da ƙarshen al'amarina» da abinda al'amarina yake komawa zuwa gare shi, ko ca ya yi: «a cikin magaggaucin al'amarina da majinkircinsa» a duniya da lahira; «to Ka ƙaddara mini shi» Ka tanade shi Ka zartar da shi «gareni», kuma ka sawwaƙe shi «Ka sawwaƙe shi gareni», «sannan Ka yi albarka» kuma Ka yawaita alheri «gareni a cikinsa», «idan kuma Ka sani» ya Allah «cewa wannan al'amarin» wanda na baka zaɓi a kansa «sharri ne gareni a cikin Addini na da rayuwata da karshen al'amarina - ko cewa ya yi : A cikin magaggaucin al'amarina da majinkircinsa - to Ka juyar da shi daga gareni nima ka juyar da ni daga gare shi , kuma Ka kaddara mini alheri a duk inda yake, sanann Ka yardar da ni da shi" da ma dukkan hukuncinKa daga abinda ka so da kabinda nake so da kuma abinda nake ki».فوائد الحديث
Tsananin kwaɗayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan koyar da sahabbansa - Allah Ya yarda da su - wannan sallar; dan abinda ke cikinta na anfani mai girma.
An so yin Istikhara da addu'ar da aka ruwaito (daga Annabi) bayanta.
An so yin Istikhara a cikin al'amuran da aka halatta waɗanda kaikawo yake faruwa a cikinsu, kuma ba ta kasancewa a cikin al'amarin da yake wajibi ko mustahabbi; domin cewa asali shi ne aikata su, sai dai zai iya yi wu wa ya nemi zaɓi a cikin abinda ke rataye da su, kamar zaɓin abokanan tafiya a aikin Hajji ko Umra.
Wajibi da mustahabbi ba'ayin Istikhara a cikin aikata su, haramun da makruhi kuwa ba'ayin Istikhara a cikin barinsu.
Ana jinkirta addu'ar zuwa bayan sallar; saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Sannan ya ce....", idan an faɗa kafin sallama to babu laifi.
Yana wajaba akan bawa ya maida dukkan al'amuransa zuwa ga Allah, kuma wajibi ne a kansa ya kuɓuta daga dabararsa da kuma ƙarfinsa; domin cewa shi ba shi da wata dabara kuma babu wani ƙarfi sai ga Allah.
التصنيفات
Sallar Istikhara