An bani abubuwa biyar, wadanda ba a baiwa wani daga cikin (Annabawa) a gabani na ba

An bani abubuwa biyar, wadanda ba a baiwa wani daga cikin (Annabawa) a gabani na ba

Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "An bani abubuwa biyar, wadanda ba a baiwa wani daga cikin (Annabawa) a gabani na ba : An bani cin nasara ta hanyar tsoro (da ake jefawa abokan gaba) wata daya (gabanin haduwar mu), kuma an sanya mini kasa ta zama wajen yin sallah ta kuma mai tsarkakewa, don haka duk wanda sallah ta riske shi cikin al'umma ta to sai ya yi ta, kuma an halarta min ganima, ba'a taba halartawa wani kafin ni ba, kuma an bani ceto, ya kasance ana aiko Annabi zuwa ga mutanensa kadai , ni kuwa an aiko ni zuwa ga mutane baki daya".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah Ya ba shi wasu dabi'u uku (wadanda) bai bada su ga wani daga Annabwa a gabnina ba. Na farko: An bani nasara da tsoro da za'a jefa shi a cikin zukatan maƙiyana koda tsakanina da su akwai tafiyar wata. Na biyu: An sanya mana ƙasa ta zama masallacin da zamu dinga sallah a duk inda muke, kuma mai tsarkakewa da turɓaya a yayin rasa ruwa, ko gaza anfani da shi. Na uku: An halatta mana ganimomin yaƙi, sune waɗanda musulmai suke ɗiba a yaƙoƙinsu tare da kafirai. Na huɗu: An bani ceto mafi girma dan hutar da mutane daga firgicin tsayuwa a ranar Alkiyama. Na biyar: An aikoni zuwa halitta gaba ɗaya mutanensu da Aljanunsun, saɓanin Annabawa kafin ni sun kasance ana aikosu ne zuwa mutanensu ne kawai.

فوائد الحديث

Halaccin ƙididdigawar bawa ga ni'imomin da Allah da Ya yi masa dan bada labari da kuma godiya ga Allah akansu.

Falalar Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga wannan al'ummar da kuma Annabinta da waɗannan ɗabi'un.

Wajabcin yin sallah a cikin lokacinta kuma a kowane halin da ta kasance, ya aikata abinda yake da iko akansa na sharuɗɗanta da rukunanta da kuma wajibanta.

Ceton da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya keɓanta da shi tsakanin Annabwa, nau’uka ne: Na ɗayansu: Cetansa ga halitta a cikin rabe hukunci tsakaninsu.

Daga cikinsu: Cetansa a na shigar 'yan aljanna aljanna. Daga cikinsu: Cetansa na musamman ga baffansa Abu Ɗalib na a sawwaƙa wuta gare shi ba ya fita ba; domin cewa shi ya mutu kafiri.

Ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna da yawa ba'a anbacesu ba a cikin wannan hadisin daga cikinsu: An ba shi dunkulallun kalmomi, kuma an cike annabta da shi, kuma an sanya sahummu kamar sahun mala'iku, da wasunsu daga ɗabi'u.

التصنيفات

Annabinmu Muhammad SAW