إعدادات العرض
Duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce
Duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce».
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt සිංහල Kurdî தமிழ் Magyar ქართული Kiswahili Română অসমীয়া ไทย Português Српски मराठी دری አማርኛ ភាសាខ្មែរالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa rayuwar duniya ga mumini kamar kurkuku ce dan wajibci ga abubuwan da shari'a da aka ɗora masa, na aikata abinda aka yi umarni da shi da kuma barin abinda aka yi gargaɗi da shi, idan ya mutu ya huta daga wannan kuma zai koma zuwa ga abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi masa tanadi na ni'ima madawwamiya. ita (duniyar) kamar kuma aljanna ce ga kafiri; domin cewa shi yana aikata dukkanin abinda ransa yake sha'awarsa kuma son ransa yake umartarsa, idan ya mutu zai juya zuwa ga abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yimasa tanadi a ranar alƙiyama na azaba tabbatacciya.فوائد الحديث
Nawawi ya ce: Dukkan mumini abin sawa a cikin kurkuku ne abin hana wa sha'awowin da aka haramta da waɗanda aka karhanta a duniya ne, kuma abin ɗorawa ayyukan ɗa'a ne masu wahala, idan ya mutu ya huta daga wannan, kuma ya koma zuwa ga abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi masa tanadi na ni'ima madawwamiya, da kuma hutu tsarkakakke daga tawaya.
Amma kafiri kawai yana da abinda ya samu a duniya tare da ƙarancinsa da kuma gurɓatarsa da abubuwan da suke ɓata su, idan ya mutu zai tafi zuwa ga azaba madawwamiya, da kuma taɓewa ta har abada.
Sindi ya ce: Faɗinsa: (Kurkukun mumini ce) cewa shi koda ya kasance a cikin ni'ima to aljanna ce mafi alheri gare shi, (Kuma aljannar kafiri ce) cewa shi ko da ya kasance a cikin wahala to wuta ita ce mafi sharri ce gare shi.
Wulaƙantar duniya ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
Duniya gidan jarraba ce ga masu imani.
Kafiri an gaggauto da aljannarsa a duniyarsa; sai aka yi masa uƙuba da haramta aljannar lahira da kuma ni'imarta.