Babu wasu mutane da suke tashi daga wani wurin zaman da ba sa ambaton Allah a cikinsa, face sun tashi kamar mushen jaki, kuma suna masu asara

Babu wasu mutane da suke tashi daga wani wurin zaman da ba sa ambaton Allah a cikinsa, face sun tashi kamar mushen jaki, kuma suna masu asara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wasu mutane da suke tashi daga wani wurin zaman da ba sa ambaton Allah a cikinsa, face sun tashi kamar mushen jaki, kuma suna masu asara".

[Ingantacce ne] [Abu Daud Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wasu mutanen da zasu zauna a wani wurin zama sannan su tashi ba su anbaci Allah a cikinsa ba sai sun tashi kamar waɗanda suka taru akan mushen jaki ta ɓangaren ɗoyi da ƙazanta; hakan yayin da suka shagalta a cikin zance daga anbatan Allah, sai wurin zaman ya zama hasara a kansu a ranar alƘiyama da kuma tawaya da dana-sanin da zata lazimcesu.

فوائد الحديث

Abinda aka ambata na gargaɗi daga rafkana daga ambatan Allah ba mai taƙaituwa bane akan wuraren zama kawai ba, kai yana game wasunsu, alNawawi ya ce: An karhanta ga wanda ya zauna a wani wuri ya bar wurin kafin ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinsa.

Hasara mai faruwa garesu a ranar alƘiyama: Ko dai da kufcewar lada da sakamako saboda rashin fa'idantuwa daga lokaci a cikin biyayya ga Allah, kodai da zunubi da uƙuba saboda shagaltuwar lokacin da saɓon Allah.

Wannan tsoratarwar idan wannan rafkanar da abubuwan da aka halatta ne, to ta yaya da wuraren zaman da aka haramta waɗanda a cikinsu akwai giba (yi da wani) da annamimanci da wasunsu?!

التصنيفات

Falalar Zikiri