Kwatankwacin muminai a soyayyarsu da jinkansu da tausayinsu tamkar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta yi ciwo sai ragowar jikin ya dauka da rashin bacci da zazzabi

Kwatankwacin muminai a soyayyarsu da jinkansu da tausayinsu tamkar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta yi ciwo sai ragowar jikin ya dauka da rashin bacci da zazzabi

Daga Nu'uman Dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kwatankwacin muminai a soyayyarsu da jinkansu da tausayinsu tamkar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta yi ciwo sai ragowar jikin ya dauka da rashin bacci da zazzabi".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa yana wajaba halin musulmai sashinsu tare da sashi ya zama da son alheri da tausayi da taimakekeniya da taimako, da jin zafin abinda ya faru gare su na cuta kamar jiki daya ne, idan wata gaba ta yi rashin lafiya daga gare shi , sai jikin ya dauka gaba dayansa da rashin bacci da zazzabi.

فوائد الحديث

Yana kamata girmama hakkokin musulmai da kwadaitarwa akan taimakekeniyarsu da tausayin junansu.

Yana kamata soyayya da taimako su kasance tsakanin ma'abota imani.

التصنيفات

Abubuwan da suke warware Musulunci