Shugaban Istighfari

Shugaban Istighfari

Daga Shaddadu Dan Aws - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Shugaban Istighfari shi ne ka ce: Ya Allah Kai ne Ubanjina babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Kai ka halicceni, kuma ni bawanKa ne, kuma ni ina kan alkawarinKa gwargwadon ikona, ina neman tsarinKa daga sharrin abinda na aikata, ina ikirari gareKa da ni'amarKa gareni, kuma ina ikirari da zunubina, to Ka gafarta mini domin cewa babu mai gafartawa sai Kai". ya ce: "wanda ya fadeta da rana yana mai sakankancewa da ita, sai ya mutu a wannan rana kafin ya yi yammaci to yana cikin 'yan aljanna, wanda ya fadeta da daddare yana mai sakankancewa da ita sai ya mutu kafin ya wayi gari to yana cikin 'yan aljanna".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa istigfri yana da lafuzza, kuma mafificinsu mafi girmansu bawa ya ce: "Ya Allah Kai ne Ubangiji na, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Ka halicceni, ni bawanKa ne, ni kuma ina kan al'kawarinKa gwargwadon iko, ina neman tsarinKa daga sharrin abinda na aikata, ina ikirari da ni'imarKa gareni, ina ikirari da zunubina, Ka gafarta mini, domin babu mai gafarta zunubai sai kai" Sai bawa ya tabbatarwa Allah da Tauhidi a farko, kuma cewa Allah ne Mahaliccinsa kuma abin bautarsa, cewa shi yana kan abinda ya yi wa Allah - tsarki ya tabbatar maSa - alkawari akansa na imani da Shi da biyayya gareShi, gwargwadan ikonsa; Domin bawa duk yadda ya tsaya akan ibada ba shi da ikon ya zo da dukkanin abinda Allah Ya umarce shi da shi da abinda yake wajaba na godiyar ni'ima, kuma cewa shi yana fakewa ne ga Allah, yana neman tsari daShi, cewa Shi abin neman tsari ne daShi daga sharrin da bawa ya aikata shi , Kuma cewa shi ya yi ikirari ya tabbatar gare shi ya yarda da ni'imarSa gare shi, kuma ya komawa kansa da ikirari da tabbatarwa da laifinsa da sabonsa. Bayan wannan kamun kafar zuwa ga Allah, ya roki Ubangijinsa Ya gafarta masa ta hanyar suturta zunubansa Ya kare shi laifukansu, da rangwamenSa da falalarSa da rahamarSa, cewa ba mai gafarta zunubai sai Shi - Mai girma da daukaka -. Sannan tsira da aminci ya bada labarin cewa su suna daga zikiran safiya da dare, wanda ya fadesu da sakankancewa da halarto ma'anoninsu da imani da su a farkon yininsa, tsakanin bullowar rana zuwa karkacewarta, shi ne lokacin rana, sai ya mutu, zai shiga aljanna, wanda ya karantata da daddare, shi ne daga faduwar rana zuwa bullowar alfijir, sai ya mutu kafin ya wayi gari, zai shiga aljanna.

فوائد الحديث

Sigogin istigafri sun saba, sashinsu sun fi sashi.

Cewa yana kamata ga bawa ya yi kwadayi akan rokon Allah da wannan addu'ar; Domin ita ce shugaban istigafari.

التصنيفات

Zikirin Safiya da Maraice