Wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, baShi da abokin tarayya, kuma cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, na yadda da Allah Shi ne Ubangiji kuma (Annabi) Muhammad Manzo ne, kuma Musulunci shi ne Addini.…

Wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, baShi da abokin tarayya, kuma cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, na yadda da Allah Shi ne Ubangiji kuma (Annabi) Muhammad Manzo ne, kuma Musulunci shi ne Addini. Za’a gafarta masa zunubinsa

Daga sa'ad Dan Abu Wakkas - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya ce: "Wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, baShi da abokin tarayya, kuma cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, na yadda da Allah Shi ne Ubangiji kuma (Annabi) Muhammad Manzo ne, kuma Musulunci shi ne Addini. Za’a gafarta masa zunubinsa".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah "Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai baShi da abokin tarayya" wato: Ina tabbatarwa ina bada labarin cewa babu wani abin bautawa da agskiya sai Allah, kuma dukkan wani abin bauta wanda ba shi ba to shi karya ne, "Kuma cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne" wato: shi bawa ne ba'a bauta masa, kuma Manzone ba ya karya, "Na yarda da Allah Shi ne Ubangiji" wato: Da RububiyyarSa da UluuhiyyarSa da sunayenSa da siffofinsa, "Da (Annabi) Muhammad shi ne Manzo" wato: Da dukkanin abinda aka aiko shi da shi, kuma ya isar da shi garemu, "Da Musulunci" wato: Da dukkanin hukunce-hukuncen Musulunci na umarni da hani, "Addini" wato: A kudircewa da aikatawa, "Za'a gafarta masa zunubinsa" wato: kananunsu.

فوائد الحديث

Maimaita wannan addu'ar a lokacin jin kiran sallah yana daga masu kankare zunubai.

التصنيفات

Kiran Sallah da Iqama, Kiran Sallah da Iqama