Ku saurara lallai cewa giya haƙiƙa an haramtata

Ku saurara lallai cewa giya haƙiƙa an haramtata

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi ya ce: Na kasance ina shayar da mutane ( giya) a gidan Abu Ɗalha, kuma giyarsu ta kasance a wannan lokacin ita ce tsimi, sai a (Cakuɗa bushasshen dabino da 'ya'yan dabino kafin su zama ɗanye) Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci wani mai kira ya yi kira: Ku saurara lallai cewa giya haƙiƙa an haramtata, ya ce: Sai Abu Ɗalha ya ce da ni: Ka fita ka zubar da ita, sai na fita sai na zubar da ita, sai ta kwaranya a lungunan Madina, sai wasu cikin mutane suka ce: Haƙiƙa an kashe wasu mutane alhali ita tana cikin cikinsu, sai Allah Ya saukar da: {Babu laifi ga waɗanda suka yi imani kuma suka aikata aiki na gari a abinda suka ɗanɗana} [al-Ma'ida: 93] karanta ayar har ƙarshenta.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa shi ya kasance yana cikin shayar da wanda yake cikin gidan mijin babarsa Abu Ɗalha - Allah Ya yarda da shi -, giyarsu ta kasance a wannan lokacin ita ce tsimi, shi ne cakuɗa bushasshen dabino da 'ya'yansa kafin ya zama ɗanye, sai ga mai kira daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kira: Ku saurara lallai cewa giya haƙiƙa an haramtata, ya ce: Sai Abu Ɗalha ya ce da ni: Ka fita, ka zubar da ita, sai na fita sai na zubar da ita, sai giyar ta kwarara a lungunan Madina, sai wasu daga mutane suka ce: Haƙiƙa an kashe (a jihadi) wasu sahabbai kafin haramtata alhali ita tana cikin cikinsu, sai Allah Ya saukar da: {Babu laifi akan waɗanda suka yi imani kuma suka aikata aiki na gari a abinda suka dandana} [al-Ma'ida: 93] Aya. Wato: Babu zunubi akan waɗanda suka yi imani a cikin abinda suka dandana kuma suka sha na giya kafin haramtata.

فوائد الحديث

Falalar Abu Ɗalha da sahabbai - Allah Ya yarda da su -, dan sun amsa umarnin Allah da gaggawa kuma ba tare da tambaya ba, wannan shi ne abinda ya kamata ga musulmi na gaskiya.

Giya: Ita Suna ne da ya ƙunshi dukkan abin da yake sa maye.

Fadikh: wani abin sha ne da ake yinsa daga 'ya'yan dabino da kuma bushasshensa ba tare da wuta ta taɓa shi ba, Busr kuwa: Shi ne 'ya'yan dabino kafin ya zama ɗanye.

Ibnu Hajar ya ce: Muhallab ya ce: Kawai an zubar da giyar ne a hanya dan bayyanar da ƙiyayyarta da kuma bayyanar da barinta, hakan ya fi rinjaye a maslaha daga cutuwa da zubar da ita a hanya.

Bayanin rahamar Allah ga bayinSa, kuma cewa Shi ba Ya yin hisabi akan aiki kafin saukar da hukunci.

Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya haramta giya; dan abinda ke cikinta na nau’ukan barna da zasu sa cuta ga hankali da kuma dukiya, saboda da ita ne mutum yake aikata zunubai da yawa; dan gushewar hankalinsa.

التصنيفات

Dalilan Saukar Ayoyi, Abubuwan Shan da aka Haramta