Zinare da zinare, azirfa da azirfa, alkama da alkama, sha'ir da sha'ir, dabino da dabino. gishiri da gishri, (dole su zama) tamka da tamka, daidai da daidai (a lokacin da za’a yi canji), idan waɗannan jinsinan suka canza, to ku siyar yadda kuke so idan ya zama hannu da hunnu ne

Zinare da zinare, azirfa da azirfa, alkama da alkama, sha'ir da sha'ir, dabino da dabino. gishiri da gishri, (dole su zama) tamka da tamka, daidai da daidai (a lokacin da za’a yi canji), idan waɗannan jinsinan suka canza, to ku siyar yadda kuke so idan ya zama hannu da hunnu ne

Daga Ubadah ɗan Samit - Allah Ya yarda da shi - yace: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Zinare da zinare, azirfa da azirfa, alkama da alkama, sha'ir da sha'ir, dabino da dabino. gishiri da gishri, (dole su zama) tamka da tamka, daidai da daidai (a lokacin da za’a yi canji), idan waɗannan jinsinan suka canza, to ku siyar yadda kuke so idan ya zama hannu da hunnu ne".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana hanyar yin inagntaccen ciniki a cikin nau’ukan da riba take shiga cikinsu (abubuwa) guda shida sune: Zinare, da azirfa, da alkama, da sha'ir, da dabino, da gishiri, idan sun kasance daga irin nau'in ne kamar saida zinare da zinare azirfa da azirfa... to babu makawa daga sharuɗɗa biyu: Na farko: Tabbatar daidaituwa a cikin awon sikeli ne, idan ya kasance abin aunawa ne na sikeli kamar zinare da azirfa, ko samun daidaito a awo idan ya kasance abin aunawa ne na kwano kamar alkama da sha'ir da dabino da kuma gishiri. Na biyu: Mai siyen ya karɓi abin siyarwar shi kuma mai siyarwar ya karɓi kuɗin, hakan (ya zama) a gurin da akayi cinikin. Idan waɗannan nau’ukan suka saɓa kamar saida zinare a bada azirfa, da dabino a bada alkama misali, to cinikin ya halatta da sharaɗi ɗaya, shi ne mai siyarwar ya karɓi kuɗin shi kuma mai siyen ya karɓi abin siyan a gurin da aka yi cinikin, inba haka bafa to cinikin ɓatacce ne, kuma sun faɗa cikin ribar da aka haramta, mai siyen da mai siyarwar duk ɗaya ne a hakan.

فوائد الحديث

Bayanin dukiyoyin da riba take shiga cikinsu da kuma yadda ciniki yake kasancewa a cikinsu.

Hani daga cinikin riba.

Takardun kuɗi suna da hukuncin zinare da azirfa a cikin illar riba.

Siye da siyarwar nau’ukan da riba take shiga cikinsu guda shida suna da halaye:

1- A saida abinda riba take shiga cikinsa da abinda riba take shiga cikinsa daga jinsinsa, kamar zinare da zinare dabino da dabino... to dan (cinikin) ya zama ingantacce an sharɗanta sharuɗɗa biyu: Samun daidaituwa a cikin awon sikeli ko awon kwano, da kuma karɓa a gurin da aka yi cinikin.

2- A saida abinda riba take shiga cikinsa da abinda riba take shiga cikinsa wanda ba jinsinsa ba tare da cewa illar ta zama iri ɗaya, kamar zinare da azirfa, da alkama da sha'ir to a hakan an sharɗanta karɓa, banda samun daidaituwa.

3- A saida abinda riba take shiga cikinsa da abinda riba take shiga cikinsa wanda bana jinsinsa ba tare da samun banbancin illar, to a hakan ba'a sharɗanta karɓa ko daidaituwa ba kamar saida zinare da dabino.

Siyrawa da siyan nau’uka waɗanda riba bata shiga cikinsu, ko ɗayansu riba na shiga cikinsa ɗayan kuma riba bata shiga cikinsa; to ba'a sharɗanta komai ba, ba hannu da hannu ba ba kuma daidaito a awo ba, kamar saida fili da zinare.

التصنيفات

Riba