Lallai Shaiɗan haƙiƙa ya yanke ƙaunar masu sallah su bauta masa a tsibirin larabawa, sai dai a sa gaba a tsakaninsu

Lallai Shaiɗan haƙiƙa ya yanke ƙaunar masu sallah su bauta masa a tsibirin larabawa, sai dai a sa gaba a tsakaninsu

Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai Shaiɗan haƙiƙa ya yanke ƙaunar masu sallah su bauta masa a tsibirin larabawa, sai dai a sa gaba a tsakaninsu".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa lallai Iblis ya yanke ƙaunar muminai masu sallah su dawo bautarsa da yi wa gunki sujjada a cikin tsibirin larabawa, sai dai cewa shi bai gusheba yana kwaɗayi, kuma bai gusheba ƙoƙarinsa da wahalarsa da tafiyarsa ba ta gushe ba a cusa rigingimu a zukatansu da gaba da yaƙe-yaƙe da fitintinu da makancin wannan a tsakaninsu.

فوائد الحديث

Bautar Shaiɗan (ita ce ) bautar gunki; domin cewa shi ne mai umarni da ita kuma mai kira zuwa gareta, saboda dalilin faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki - game da (Annabi) Ibrahim - aminci ya tabbata agare shi -: (Ya babana kada ka bautawa Shaiɗan...).

Shaiɗan yana iya ƙoƙari a afkar da rigingimu da gaba da yaƙe-yaƙe da fitintinu tsakanin musulmai.

Daga fa'idojin sallah a Musulunci cewa ita tana tsare soyayya tsakanin musulmai, kuma tana ƙarfafa alaƙar 'yan uwantaka tsakaninsu.

Sallah ita ce mafi girman alamomin Addini bayan shaida biyu, saboda haka ne aka saki sunan musulmai (da) masu sallah.

Tsibirin Larabawa yana da wasu keɓantattun abubuwa banda waninsa cikin garuruwa.

Idan an ce haƙiƙa bautar gumaka ta faru a wasu daga sashin tsibirin Larabawa, alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: (Lallai Shaiɗan ya yanke ƙaunar cewa masu sallah su bauta masa...), to wannan labartawa ne game da abinda ya afku a cikin ran Shaiɗan na yanke ƙauna saboda abinda ya gani na nasarori, da shigar mutane a cikin Addinin Allah jama'a - jama'a, hadisin ya labarta ne game da zatan Shaiɗan da abinda yake sa ran zai afku, sannan waƙi'i (ya zama) saɓanin hakan dan wata hikimar da Allah - Mai girma da ɗaukaka - yake nufinta.

التصنيفات

Munanan Halaye