Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya fito daga bayan gida yana cewa: "Ina neman gafararKa

Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya fito daga bayan gida yana cewa: "Ina neman gafararKa

Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya fito daga bayan gida yana cewa: "Ina neman gafararKa".

[Ingantacce ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Buhari ne ya rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi - Al-Darumi Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya fito daga biyan buƙatarsa na bayan gida yana cewa: Ina roƙonKa (gafararKa) ya Allah.

فوائد الحديث

An so faɗin: "Ina neman gafafarKa" bayan fitowa daga wurin biyan buƙata.

Neman gafarar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi ga Ubangijinsa a dukkanin halaye.

An ce: A cikin sababin neman gafara bayan biyan buƙata: Don taƙaitawa ne a cikin godiyar ni'imomin Allah masu yawa , daga cikinsu akwai sawwaƙa fitar abinda yake cutarwa, kuma ina neman gafararKa dan na shagalta daga anbatanKa a lokacin biyan buƙata.

التصنيفات

Ladaban biyan bukata