Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum ya yi sallah shi kaɗai a bayan sawu, sai ya umarce shi ya sake sallar

Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum ya yi sallah shi kaɗai a bayan sawu, sai ya umarce shi ya sake sallar

Daga Wabisah - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum ya yi sallah shi kaɗai a bayan sawu, sai ya umarce shi ya sake sallar.

[Hasan ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum ya yi sallah shi kaɗai a bayan sawu, sai ya umarce shi ya sake sallarsa; domin sallarsa ba ta inganta ba a wannan halin.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa akan gaggawar zuwa sallar jam’i da halartarta, kuma kada ya yi sallah a bayan sawu shi kaɗai dan kada ya bijirar da sallarsa ga ɓaci.

Ibnu Hajar ya ce: Wanda ya fara sallah shi kaɗai a bayan sawu sannan ya shiga cikin sawu kafin ɗagowa daga ruku'u to sakewa ba ta wajaba gare shi ba, kamar yadda yake a cikin hadisin Abu Bakrata, inba haka ba to yana wajaba abisa gamewar hadisin Wabisah.

التصنيفات

Hukunce Hukuncen limami da Mamu