Hukunce Hukuncen limami da Mamu

Hukunce Hukuncen limami da Mamu

7- "Idan za ku yi sallah, to, ku daidaita sahunku, sannan ɗayanku ya yi muku limanci, idan ya yi kabbara sai ku yi kabbara*, idan ya ce: {Ba waɗanda ka yi fushi da su ba, ba kuma ɓatattu ba} [Al-Fatiha: 7], sai ku ce: Ameen, Allah zai amsa muku, idan ya yi kabbara ya yi ruku'u, sai ku yi kabbara ku yi ruku'u, domin cewa liman yana yin ruku'u ne kafinku, kuma yana ɗagowa ne kafinku", sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Waccan da waccan, idan ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, sai ku ce: Ya Allah Ubangijinmu godiya ta tabbata gareKa, Allah Zai jiye muku (wato Zai amsa); domin cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya faɗa a kan harshen AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, idan ya yi kabbara ya yi sujjada sai ku yi kabbara sai ku yi sujjada, domin cewa liman yana yin sujjada ne kafinku kuma yana ɗagowa ne kafinku", sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Waccan da waccan, idan an zo wurin zama; to, farkon abin da ɗayanku zai faɗa (shi ne): gaisuwa ta tabbata ga Allah tsarkakan salloli sun tabbata ga Allah, aminci ya tabbata a gareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata a garemu da bayin Allah nagari, ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ina shaida cewa (Annabi) muhammadu bawanSa ne, kuma manzonSa ne".