Shin dayanku ba ya jin tsoron idan ya dago kansa kafin liman, Allah Ya maida kansa kan jaki ko Allah Ya maida surarsa surar jaki

Shin dayanku ba ya jin tsoron idan ya dago kansa kafin liman, Allah Ya maida kansa kan jaki ko Allah Ya maida surarsa surar jaki

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin dayanku ba ya jin tsoron idan ya dago kansa kafin liman, Allah Ya maida kansa kan jaki ko Allah Ya maida surarsa surar jaki".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana narko mai tsanani akan wanda ya dago kansa kafin limaminsa, Allah Ya maida kansa kan jaki, ko Ya maida surar halittarsa ta zama surar jaki.

فوائد الحديث

Akwai halaye hudu ga mamu tare da liman: Uku an hana, su ne: Rigayarsa da daidai da shi da jinkirta masa.

Abinda ya halatta ga mamu: Bin liman.

Wajabcin mamu ya bi liman a sallah.

Narko da canja surar wanda yake dago kansa kafin liman zuwa surar jaki abu ne mai yiwuwa, shi ne shafewa.

التصنيفات

Hukunce Hukuncen limami da Mamu