ku daidaita sahunku, don daidaita shahu na daga cikar sallah

ku daidaita sahunku, don daidaita shahu na daga cikar sallah

Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "ku daidaita sahunku, don daidaita shahu na daga cikar sallah".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana umartar masu yin sallah kan su daidaita sahunsu, kuma kada sashinsu ya gabata akan sashi kada kuma ya jinkirta, kuma daidaita sahu yana daga cikar sallah , kuma karkace sahu ɓaci ne da tawaya a sallah.

فوائد الحديث

Halaccin kula da dukkan abinda yake cika sallah kuma yake nisantar da ita daga tawaya.

Hikimar annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a koyarwa, ta inda ya haɗa hukunci tare da dalilinsa; dan bayyanar da hikimar shar'amtawa, da nishaɗantar da rayuka akan kamantawa.

التصنيفات

Hukunce Hukuncen limami da Mamu, Hukunce Hukuncen limami da Mamu, Hukunce Hukuncen Masallaci, Hukunce Hukuncen Masallaci