إعدادات العرض
Ya Manzon Allah, dukiyoyi sun halaka hanyoyi sun yanke, ka roƙa mana Allah Ya shayar da mu
Ya Manzon Allah, dukiyoyi sun halaka hanyoyi sun yanke, ka roƙa mana Allah Ya shayar da mu
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya shiga masallaci a ranar Juma'a ta wata ƙofar da ta kasance daura da gidan hukunci, alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana tsaye yana huɗuba, sai ya fuskanci Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tsaye, sannan ya ce: Ya Manzon Allah, dukiyoyi sun halaka hanyoyi sun yanke, ka roƙa mana Allah Ya shayar da mu, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ɗaga hannayensa, sannan ya ce: «Ya Allah Ka shayar da mu, ya Allah Ka shayar da mu, ya Allah Ka shayar da mu» Anas ya ce: Na rantse da Allah bama ganin wani girgije ko wani yanki na girgije kuma tsakaninmu da Sal'a babu wani ɗaki ko gida, ya ce: Sai wani girgije ya ɓullo ta bayanmu kwatankwacin garkuwa, lokacin da ya tsaya a tsakiyar sama sai ya yaɗu, sannan ya zubar da ruwa, na rantse da Allah, bamu ga rana ba tsawon kwana shida, sannan wani mutum ya shigo daga waccan ƙofar a wata Juma'ar, alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana tsaye yana huɗuba, sai ya fuskance shi a tsaye, sai ya ce: Ya Manzon Allah, dukiyoyi sun halaka, hanyoyi sun yanke, ka roƙa mana Allah Ya ɗauke mana ruwan, ya ce: Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ɗaga hannayensa, sannan ya ce: «Ya Allah Ka saukar da ruwan a gefenmu ba akanmu ba, ya Allah akan tuddai da duwatsu, da cikin kwarrai, da matsirar bishiyoyi» ya ce: Sai ya ɗauke, sai muka fita muna tafiya cikin rana, Sharik ya ce: Na tambayi Anas ɗan Malik: Shin shine mutumin nan na farko? sai ya ce: «Bansani ba».
الترجمة
العربية Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Português Kurdî دری বাংলা Македонски Magyar Tiếng Việt ქართული ไทย অসমীয়াالشرح
Wani balaraben ƙauye ya shiga cikin masallacin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a ranar Juma'a ta ƙofar da ke kudancin masallaci daura da gidan Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -, alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana tsaye yana huɗuba, sai mutumin ya fuskanci Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma ya ce: Ya Manzon Allah, dabbobi sun halaka, hanyoyi sun yanke saboda mutuwar dabbobin da suke ɗaukar mutane ko sun yi rauni saboda yunwa, to ka roƙa mana Allah Ya shayar da mu ruwa. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ɗaga hannayensa, sannan ya ce: Ya Allah Ka shayar da mu, ya Allah Ka shayar da mu, ya Allah Ka shayar da mu. Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wallahi ba ma ganin ko da wani yanki na girgije daga sama, kuma tsakaninmu a cikin masallaci da dutsen Sal'a a yammacin masallaci inda ta ɓangarensa ne girgijen ya zo babu wani ɗaki ko gida da zai karesu daga ganinsa. Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Sai wani kewayayyen girgije kwatankwacin garkuwa ya ɓullo shi ne ƙaramin faranti, lokacin da ya tsaya a tsakiyar saman Madina sai ya yaɗu, sannan ya zubar da ruwa, na rantse da Allah, bamu ga rana ba saboda ruwan har wata Juma'ar daban, inda wancan mutumin ya shiga ta waccar ƙofar, alhali shi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana tsaye yana huɗuba, sai ya fuskance shi yana tsaye, sai ya ce: Ya Manzon Allah, dukiyoyi sun halaka, hanyoyi sun yanke, to ka roƙa mana Allah Ya ɗauke mana ruwan. Ya ce: Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ɗaga hannayensa, sannan ya ce: Ya Allah Ka juyar da ruwan a gefanmu ba'a kanmu ba, ya Allah akan abin da ya ɗago daga ƙasa kamar tudu, da ƙaramin dutse, da cikkunan kwari, da matsirar bishiyoyi (jijiyoyin bishiya). Anas ya ce: Sai girgijen da yake zubar da ruwan ya yanke, sai muka fita muna tafiya cikin rana.فوائد الحديث
Aikata sabubba dan neman arziƙi, na addu'a, da tafiya a cikin ƙasa, ba ya kore dogaro ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
An so addu'a da wannan addu'ar ta Annabi dan neman ruwa.
Halaccin neman gari ya yi wasai - neman gari ya yaye da kuma daukewar ruwa - a lokacin cutuwa da ruwan, kuma an keɓanci wanzuwar ruwan saman akan tuddai da duwatsu da cikin kwari; domin cewa su ne suka fi dacewa da shuka da kuma kiwo.
Halaccin neman addu'a daga waɗanda ake zatan salaha da taƙawa a tare da su daga rayayyu waɗanda ke halarce, wannan tawassulin ya halatta, amma yin tawassuli da alfarmar wani daga cikin ababen halitta, a raye yake ko a mace, to wannan ba ya halatta; domin hakan yana daga cikin hanyoyin shirka.
Halaccin nacewa a cikin addu'a da kuma maimaitata.
Halaccin yi wa mai yin huɗuba magana a ranar Juma'a don buƙata.
Bayyanar ikon Allah a zahiri akan saukar ruwan da kuma ɗauke shi.
Hikimar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da yin addu'a da ɗauke ruwan ga wanda yake a cikinsa akwai cutarwa banda wanda babu cutarwa a cikinsa
Halaccin neman sha da fari a cikin huɗuba.
Ɗaga hannaye a cikin addu'a; domin a cikin hakan akwai ma'anar buƙatuwa, da kuma kardadon ma'anar bayarwa a hakan, haƙiƙa malamai sun yi ijma'i akan ɗaga hannaye a wannan lokacin.
Aya daga cikin ayoyin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, mai nuni akan Annabtarsa, haƙiƙa an amsa addu'arsa a wannan halin, a kan zuwan ruwan saman da kuma ɗauke shi.
التصنيفات
Sallar Roqon Ruwa