Ya Ubangiji ina roƙonKa shiriya da tsoron Allah, da kamewa, da wadata

Ya Ubangiji ina roƙonKa shiriya da tsoron Allah, da kamewa, da wadata

Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana cewa: «Ya Ubangiji ina roƙonKa shiriya da tsoron Allah, da kamewa, da wadata».

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Ya kasance daga addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Ya Allah ni ina roƙonKa shiriya» hanya madaidaiciya na sanin gaskiya da aiki da ita. «Da tsoron Allah», ruko da umarni da nisantar hane-hane. «Da kamewa» kamewa daga abinda ba ya halatta kuma ba shi da kyau na magana ne ko aiki. «Da wadatuwa» daga halitta, inda ba zai yi buƙatuwa ba zuwa ga wani inba Uabngijinsa - Mai girma da ɗaukaka ba -.

فوائد الحديث

Ɗaukakar waɗannan ɗabi'un: Shiriya da tsoron Allah da kamewa da wadata, da kwaɗaitarwa akan ɗabi'antuwa da su.

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya mallakawa kansa wani amfani ko cutarwa, wanda yake mallakar hakan Shi ne Allah - Maɗaukakin sarki -.

Wanda yake mallakar amfani da cutarwa da shiryar da halitta Shi ne Allah Shi kaɗai, ba wani mala'ika makusanci ba kuma ba wani Annabi abin aikowa ko waninsu ba.

التصنيفات

Addu’o’I da aka samu daga Annabi