Tsarki ya tabbata ga Allah da yabonSa, za a dasa masa bishiyar dabino a cikin aljanna

Tsarki ya tabbata ga Allah da yabonSa, za a dasa masa bishiyar dabino a cikin aljanna

Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Tsarki ya tabbata ga Allah da yabonSa, za a dasa masa bishiyar dabino a cikin aljanna».

[Ingantacce ne] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Tsarki ya tabbata ga Allah) Ya tsarkakeShi (Mai girma) da zatinSa da siffofinSa da kuma ayyukanSa (da yabonSa) abin haɗawa da raɓa siffofin cika gareShi - tsarki ya tabbatar maSa -; za'a kafa kuma za'a dasa masa wani dabino a cikin ƙasar aljanna a duk lokacin da ya faɗeta.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa akan yawaita ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -, daga hakan (akwai): Tasbihi tare da Tahmidi.

Aljanna mai yalwa ce, kuma dashenta shi ne Tasbihi da Tahmidi, wannan falala ce daga Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma ni'imominSa.

An keɓanci bishiyar dabino a cikin hadisin banda waninta cikin bishoyoyi; saboda yawan anfaninta da kuma daɗin 'ya'yanta; sbaoda haka ne Allah Ya buga misalin mumini da kuma imaninsa da ita a cikin Alƙur'ani.

التصنيفات

Fa’idojin Ambaton Allah Maigirma da xaukaka