إعدادات العرض
Mun yi sahur tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan ya tashi zuwa sallah, na ce: Nawa ne tsakanin kiran sallah da sahur? ya ce: Gwargwadan ayoyi hamsin
Mun yi sahur tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan ya tashi zuwa sallah, na ce: Nawa ne tsakanin kiran sallah da sahur? ya ce: Gwargwadan ayoyi hamsin
Daga Zaidu ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun yi sahur tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan ya tashi zuwa sallah, na ce: Nawa ne tsakanin kiran sallah da sahur? ya ce: Gwargwadan ayoyi hamsin.
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Bahasa Indonesia Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Français Tiếng Việt සිංහල Português Kurdî Русский Kiswahili অসমীয়া ગુજરાતીالشرح
Wasu daga sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun yi sahur tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tashi zuwa sallar Asuba. Sai Anas ya cewa Zaid ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi -: Nawane gwargwadan lokaci sahur tsakanin kiran sallah da iƙama? Sai Zaid ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Gwargwadan karanta ayoyi hamsin ne matsakaita, ba dogwaye ba ba kuma gajeru ba, ba karatu da gaggawa ba ba kuma a hankali ba.فوائد الحديث
Falalar jinkirta sahur har zuwa gab da Asuba; domin idan ya jinkirta to anfanin jikin daga gare shi ya fi girma kuma anfaninsa a yinin ya fi yawa.
Kwaɗayin sahabbai da haɗuwa da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan su yi koyi da shi.
Kyakkyawar mu'amalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga sahabbansa, inda ya kasance yana cin (abin ci) tare da su.
Lokacin kamewa shi ne ɓullowar alfijir.
Faɗinsa: "Nawa ne tsakanin kiran sallah da sahur", abin nufi tsakanin sahur da iƙama; saboda faɗinsa a wani hadisn: "Nawa ne tsakanin gamawarsu daga sahur ɗinsu da kuma shigarsu sallah", hadisai sashinsu suna fassara sashi.
AlMuhallab ya ce: A cikinsa akwai ƙaddara lokuta da ayyukan jiki, larabawa sun kasance suna ƙaddara lokuta da ayyuka kamar faɗinsu: Gwargwadan tatsar nonon akuya, da gwargwadan soke raƙumi, sai Zaid ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi - ya kauce daga hakan zuwa ƙaddarawa da karatu; dan nuni zuwa cewa wancan lokacin ya kasance lokacin ibada ne da karatu, da sun kasance suna ƙaddarawa da wanin aiki da ya ce misali: Gwargwadan daraja, ko ɗaya bisa uku ɗaya bisa biyar na awa.
Ibnu Abi Jamrah ya ce: Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance yana duba abinda shi ne mafi sauƙi ga al'ummarsa sai ya aikata shi; domin cewa shi da bai yi sahur ba da sun bi shi sai ya yi wa wasunsu wahala, da kuma ya yi sahur a tsakiyar dare da ya yi wa wanda bacci yake rinjayarsa wahala zai iya kai shi zuwa barin sallar Asuba ko ya buƙatu zuwa ƙoƙarin rashin bacci.
التصنيفات
Sunnonin Azumi