Banu Isra'il sun kasance Annabawa ne suke shugabantarsu, duk lokacin da wani Annabi ya rasu sai wani Annabin ya maye gurbinsa, lallai cewa babu wani Annabi a baya na, za'a samu halifofi zasu yawaita

Banu Isra'il sun kasance Annabawa ne suke shugabantarsu, duk lokacin da wani Annabi ya rasu sai wani Annabin ya maye gurbinsa, lallai cewa babu wani Annabi a baya na, za'a samu halifofi zasu yawaita

Daga Abu Hazim ya ce: Na zauna da Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - shekara biyar, sai na ji shi yana zantarwa daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce; "Banu Isra'il sun kasance Annabawa ne suke shugabantarsu, duk lokacin da wani Annabi ya rasu sai wani Annabin ya maye gurbinsa, lallai cewa babu wani Annabi a baya na, za'a samu halifofi zasu yawaita" Suka ce: Da me zaka umarce mu? ya ce: "Ku cika caffar na farko sai na farko, ku basu haƙƙinsu, domin cewa Allah Mai tambayarsu ne daga abinda Ya basu kiwo".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Banu Isra'il sun kasance Annabawa ne suke shugabantar su, suna jiɓintar al'amuransu kamar yadda sarakuna da shugabanni suke aikatawa da talakawansu, a duk lokacin da ɓarna ta bayyana a cikinsu sai Allah Ya aiko musu da wani Annabin da zai daidaita al'amarinsu kuma ya gusar da abinda suka canja na hukunce-hukunce. Lallai cewa babu wani Annabi a bayana (ballantana) ya aikata abinda waɗancan suke aikatawa, za'a samu halifofi a bayana zasu yawaita kuma jayayya da saɓani zasu faru a tsakaninsu. Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Da me zaka umarce mu? Sai ya ce: Idan Aka yi wa halifa caffa bayan wani halifan; to caffar na farko ce ingantacciya wajibine a cikata, caffar na biyun kuma ɓatacciya ce kuma nemanta yana haramta, kuma ku basu haƙƙinsu, ku bisu ku yi mu'amala da su da ji da bi inba a saɓon ba ne, domin cewa Allah Zai tambayesu kuma Zai yi musu hisabi a kan abinda suke aikata shi gareku.

فوائد الحديث

Babu makawa ga talakawa daga wani Annabi ko halifa da zai tsayu da al'amarinsu, kuma zai ɗorasu akan hanya madaidaiciya.

Cewa babu wani Annabi bayan Annabinmu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Gargaɗarwa daga fito na fito akan wanda shugabancinsa ya tabbata ta hanya ta shari'a.

Ba ya halatta a yi caffa ga halifofi biyu a lokaci ɗaya.

Girman nauyin shugaba, domin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai yi masa hisabi game da talakawansa.

Ibnu Hajar ya ce: Gabatar da al'amarin Addini akan al'amarin duniya; domin cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da cika haƙƙin shugaba dan abinda ke cikinsa na ɗaukaka kalmar Addini da kame fitina da sharri; da jinkirta al'amarin nema da haƙƙinsa ba zai sarayar da shi ba, haƙiƙa Allah Ya yi masa alƙawari cewa Shi Zai tseratar da shi kuma zai cika masa koda a gidan lahira ne.

Alama ce daga alamomin Annabcinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, haƙiƙa halifofi sun yawaita a bayansa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma masu gyarawa da masu munanawa sun jerantu ga al'umma.

التصنيفات

Qissosi da labaran Al-umman da suka gabata