Lallai Ubangijinku Mai tsananin Kunya ne kuma Mai Karamci, yana jin kunyar Bawansa ya daga Hannayensa uwa gare shi sannan ya dawo masa da su hakan

Lallai Ubangijinku Mai tsananin Kunya ne kuma Mai Karamci, yana jin kunyar Bawansa ya daga Hannayensa uwa gare shi sannan ya dawo masa da su hakan

An karbo daga Salman-Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Lallai Ubangijinku Mai tsananin Kunya ne kuma Mai Karamci, yana jin kunyar Bawansa ya daga Hannayensa uwa gare shi sannan ya dawo masa da su hakan"

[Ingantacce ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi]

الشرح

Wannan Hadisin yana nuna Halacin daga Hannaye a wajen Addu'a, kuma lallai cewa wannan aikin sababi ne daga ikin Sababan amsa Addu'a, saboda abun da yake cikin wannan akawai sifa ta bayyana bukata da kuma kaskantar da kai daga bawa a gaban Mawadaci mai karamci, da kuma kyakyyawan fata na cewa zai sanya bukatarsa a cikinsu wacce ya ke roko ubangijinsa,saboda shi Madaukaki daga cikin kyautar sa da Karamcinsa yana jin kunyar Bawansa idan ya daga Hannayensa zuwa gare shi yana rokon sa ya dawo masa da su haka ba tare da komai na kyauta ba, saboda shi Mai yawan kyauta ne kuma mai Karamci

التصنيفات

Ladaban Addu’a