إعدادات العرض
Duk wanda yake da iko a cikinku to ya yi aure, domin cewa shi ne yafi rintse ido, kuma ya fi katange farji, wanda ba zai iya ba to na umarce shi da azimi, domin shi kariyane gare shi
Duk wanda yake da iko a cikinku to ya yi aure, domin cewa shi ne yafi rintse ido, kuma ya fi katange farji, wanda ba zai iya ba to na umarce shi da azimi, domin shi kariyane gare shi
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: "Duk wanda yake da iko a cikinku to ya yi aure, domin cewa shi ne yafi rintse ido, kuma ya fi katange farji, wanda ba zai iya ba to na umarce shi da azimi, domin shi kariyane gare shi".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Português Kurdî සිංහල অসমীয়া Kiswahili Tiếng Việt አማርኛ ગુજરાતી Nederlands پښتو नेपाली മലയാളം ไทย Svenska Кыргызча Română Malagasyالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar da wanda yake da iko akan jima'i da ɗawainiyar aure da ya yi aure; domin cewa shi yafi kiyaye gani daga haram, kuma ya fi tsananin katange farjinsa, da kuma hana afkawa cikin alfasha, wanda ba zai iya ɗaukar ɗawainiyar aure ba alhali shi yana mai iko akan jima'i to ya yin azimi domin cewa shi yana yanke sha'awar farji da sharrin maniyyi.فوائد الحديث
Kwaɗayin Musulunci akan sabubban kamewa da kuɓuta daga alfasha.
Kwaɗaitar da wanda ba zai iya ɗaukar nauyin ɗawainiyar aure ba da ya yi azimi; domin cewa shi yana raunana sha'awa.
Ta yadda ya kamanta azimi da kariya; domin kariya (dandaƙa) ita ce kwankwatsa jijiyoyin maraina, da zarar sun tafi sai sha'awar jima'i ta tafi da tafiyarsu, haka nan azimi, shi mai raunana sha'awar jima'i ne.