Ku yaƙi mushrikai da dukiyoyinku da rayukanku da kuma harsunanku

Ku yaƙi mushrikai da dukiyoyinku da rayukanku da kuma harsunanku

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yaƙi mushrikai da dukiyoyinku da rayukanku da kuma harsunanku".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da yaƙar kafirai, da yin ƙoƙari a fuskantarsu ta kowace hanya gwargwadan iko dan kalmar Allah ta zama ita ce maɗaukakiya, daga hakan: Na farko: Ciyar da dukiya a yaƙarsu; na siyan makamai da ciyarwa ga mayaƙa da makamancin hakan. Na biyu: Fita da rai da jiki dan haɗuwa da su da kuma tunkuɗesu. Na uku: Da kiransu ga wannan Addinin da harshe, da tsaida hujja akansu, da tsawatar da su da yi musu raddi.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa akan yaƙar mushrikai da rai da dukiya da kuma harshe; kowa gwargwadan ikonsa, kuma yaƙi ba ya taƙaituwa akan yaki da rai kadai.

Umarni da yaƙi na wajabci ne, zai iya zama wajibi aini (akan kowa da kowa), kuma zai iya zama wajibi kifa'i (wasu sun ɗaukewa wasu).

Allah Ya shar’anta jihadi saboda wasu al'amura daga cikinsu: Na farko: Faɗa da shirka da mushrikai; domin cewa Allah ba Ya karɓar shirka har abada.

Na biyu: Kawar da wahalhalun da suke bijirowa hanyar kira zuwa ga Allah.

Na uku: Kiyaye aƙida daga dukkan abinda yake kishiyantarta.

Na huɗu: Kariya ga musulmai da ƙasashensu da mutuncinsu da kuma dukiyoyinsu.

التصنيفات

Hukunci Jahadi