إعدادات العرض
Lallai ni na fiku tsoron Allah kuma na fiku saninSa
Lallai ni na fiku tsoron Allah kuma na fiku saninSa
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai umarce su da wasu ayyukan yana umartar su da abin da zasu iya, suka ce: Lallai mu bamu kasance kamar yanayinka ba ya Manzon Allah, lallai Allah Ya gafarta maka abin da ya gabata daga zunubinka da abin da ya jinkirta, sai ya yi fushi har sai da aka gane fushi a fuskarsa, sannan ya ce: «Lallai ni na fiku tsoron Allah kuma na fiku saninSa».
الترجمة
العربية Português دری Македонски Tiếng Việt Magyar ქართული Bahasa Indonesia বাংলা Kurdî ไทย অসমীয়া Nederlandsالشرح
Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai umarci mutane da wani aiki cikin ayyuka sai ya umarce su da abin da zai yi musu sauƙi banda wanda zai wahalar da su, dan jin tsoron kada su gajiya daga dawwama a kansa, sai ya yi aikin da shine kishiyar abin da yake umartarsu da shi daga sauƙaƙawa, sai dai cewa su sun nemi taklifin abin da zai wahalar da su daga gare shi, dan sun ƙudirce buƙatuwarsu zuwa kai matuƙa a cikin aikin dan ɗaukaka darajoji koma bayansa. Sai su ce: Lallai halinmu ba kamar halinka ba ne ya Manzon Allah, domin Allah haƙiƙa Ya gafarta maka abin da ya gabata daga zunubinka da abin da ya jinkirta, sai ya yi fushi har sai da aka gane fushi a fuskarsa, sannan ya ce: Lallai ni na fiku tsoron Allah kuma na fiku saninSa, dan haka ku aikata abin da nake umartarku da shi.فوائد الحديث
Ibnu Hajar ya ce: Kaɗai ya umarce su da abin da zai yi musu sauƙi ne dan su dawwama a kansa kamar yadda ya faɗa a ɗaya hadisn: «Mafi soyuwar aiki a wurin Allah mafi dawwamarsa».
Mutum na gari yana kamata kada ya bar ijtihadi a cikin aiki dan dogaro akan shi mutumin kwarai ne.
Halaccin mutum ya bada labarin halin da yake cikinsa na falala gwargwadan buƙatar hakan, in akwai aminci daga alfahari da kuma girmama kai.
Abin da ya fi a cikin ibada shi ne tsakatsaki da kuma lazimta, ba wuce gona da iri ba wacce zata kai zuwa bari.
Ibnu Hajar ya ce: Bawa idan ya kai ƙololuwa a cikin ibada da fa'idojinta hakan zai zama ya fi jansa zuwa lazimtarta, dan wanzar da ni'ima, da kuma neman ƙarinta ta hanyar godiya a kanta.
Halaccin fushi yayin saɓawa al'amari na shari'a, da kuma yin inkari akan mai hazaƙa wanda ya dace ga fahimtar ma'ana idan ya taƙaita a cikin fahimtar, dan kwaɗaitarwa gareshi akan farkawa.
Sauƙin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa, kuma cewa Addini mai sauƙi ne, kuma cewa shari'a miƙaƙƙiya ce mai sauƙi.
Tsananin kwaɗayin sahabbai a cikin ibada, da kuma yanda suke neman ƙarin alheri.
Tsayuwa in da mai shara'antawa ya iyakance na Azima da kuma Rukhsa, da ƙudirce cewa riƙo da mafi sauƙi wanda ya dace da shari'a ya fi daga mafi tsanani wanda ya saɓawa shari'a.
