Idan mutum ya rasu akin sa ya yanke sai dai daga abu uku: Sadaka mai gudana, ko wani ilimin da ake anfanuwa da shi, ko ɗa na gari da ya ke masa addu'a

Idan mutum ya rasu akin sa ya yanke sai dai daga abu uku: Sadaka mai gudana, ko wani ilimin da ake anfanuwa da shi, ko ɗa na gari da ya ke masa addu'a

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan mutum ya rasu akin sa ya yanke sai dai daga abu uku: Sadaka mai gudana, ko wani ilimin da ake anfanuwa da shi, ko ɗa na gari da ya ke masa addu'a".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa aikin mamaci yana yankewa da rasuwarsa,, kyawawan ayyuka basa samunsa bayan mutuwnrsa sai a waɗannan ukun; dan kasancewarsa ya zama sababinsu: Na farko: Sadakar da ladanta yake gudana kuma yake dawwama, ba mai yankewa ba, kamar waƙafi, da gina masallatai, da haƙa rijiyoyi, da wanin hakan. Na biyu: Ilimin da mutane suke anfanuwa da shi, kamar wallafa littattafan ilimi, ko kamar ya koyar da wani mutum, sai wannan mutumin ya yaɗa wannan ilimin bayan mutuwarsa. Na uku: Ɗa na gari mumini da zai yi masa addu'a.

فوائد الحديث

Ma'abota ilimi sun haɗu akan cewa daga abinda yake riskar mutum bayan mutuwarsa na lada: Sadaka mai gudana, da ilimin da ake anfanuwa da shi, da addu'a, kuma ya zo a cikin wasu Hadisan daban: Hajji kuma.

An keɓanci waɗannan ukun da ambato a cikin wannan Hadisin; domin sune tushen alheri, kuma mafi rinjayar abinda ma'abota falala suke nufin wanzuwarsa bayansu.

Dukkan ilimin da ake anfanuwa da shi to shi lada yana samuwa gare shi, sai dai ƙololuwarsu shi ne ilimi na shari'a da ilimummuka masu ƙarfafarsa.

Ilimi mafi anfani shi ne waɗannan ukun; domin ilimi mutumin da yake neman saninsa yana anfanuwa da shi, akwai kiyaye shari'a a cikin ilimi, akwai anfanar halitta a gamewa, shi ne mafi ƙunsa kuma mafi gamewa; domin shi yana neman iliminka samamme a cikin rayuwarka kuma samamme bayan mutuwarka.

Kwaɗaitarwa akan tarbiyyar yara salihai; su ne waɗanda suke anfanar iyayensu a lahira, daga anfanar su suna yi musu addu'a.

Kwaɗaitarwa akan kyautatawa mahaifa bayan mutuwarsu, shima yana daga aikin alherin ɗa zai anfana da shi.

Addu'a tana anfanar mamaci koda daga wanin ɗa ne, sai dai ankeɓanci ɗa da ambato; domin shi ne wanda yake ci gaba a addu'a ga mutum a galibi har zuwa mutuwarsa.

التصنيفات

Waqafi, Falalar Addu'a