Idan 'yan aljanna suka shiga aljanna, ya ce: Allah -Maɗaukakin sarki - zai ce: Kuna son wani abu ne da zan ƙaro muku shi?

Idan 'yan aljanna suka shiga aljanna, ya ce: Allah -Maɗaukakin sarki - zai ce: Kuna son wani abu ne da zan ƙaro muku shi?

Daga Suhaib - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan 'yan aljanna suka shiga aljanna, ya ce: Allah -Maɗaukakin sarki - zai ce: Kuna son wani abu ne da zan ƙaro muku shi? sai su ce: Ba Ka haskaka fusokinmu ba? kuma ba Ka shigar da mu aljannah ba, kuma Ka tseratar da mu daga wuta? ya ce: Sai a yaye hijabi, ba'a basu wani abu mafi soyuwa a gare su ba daga duba zuwa Ubanginsu - Mai girma da ɗaukaka -".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa idan 'yan aljanna suka shiga aljanna, Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - zai ce musu: Shin kuna son wani abu da zan ƙaro muku? Sai 'yan aljanna gaba ɗayansu su ce: Shin baKa hasakaka fuskokinmu ba? Shin baKa shigar da mu aljanna ba, kuma Ka tseratar damu daga wuta? Sai Allah Ya gusar da shamaki kuma Ya ɗauke shi; hijabinSa (shi ne) haske, ba'a basu wani abuba mafi soyuwa garesu daga duba zuwa Ubangijinsu - Mai girma da ɗaukaka ba.

فوائد الحديث

Yaye hijabi daga 'yan aljanna sai su ga Ubangijinsu, amma kafirai; to su ababen haramtawa ne daga ganin Ubangiji.

Mafi girman ni'imar aljanna (ita ce) ganin muminai ga Ubangijinsu.

Dukkan 'yan aljanna duk yadda matsayinsu ya saɓa zasu ga Ubangijinsu - Maɗaukaki -.

Falalar Allah ga muminai da shigar da su aljanna.

Muhimmancin gaggawa zuwa aljanna da ayyuka na gari da bin Allah - Maɗaukakin sarki - da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

التصنيفات

Sifar Al-janna da Wuta