إعدادات العرض
Idan ɗayanku ya farka daga baccinsa to ya face hancinsa sau uku, domin cewa Shaiɗan yana kwana akan karan hancinsa
Idan ɗayanku ya farka daga baccinsa to ya face hancinsa sau uku, domin cewa Shaiɗan yana kwana akan karan hancinsa
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya farka daga baccinsa to ya face hancinsa sau uku, domin cewa Shaiɗan yana kwana akan karan hancinsa".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt Kurdî Português සිංහල Nederlands অসমীয়া Kiswahili ગુજરાતી አማርኛ پښتو ไทย Românăالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da wanda ya farka daga baccinsa cewa ya face hancinsa sau uku; facewa ita ce fitar da ruwa daga hanci bayan shigar da shi, hakan domin cewa Shaiɗan yana kwana akan karan hanci - shi ne hancin gaba ɗayansa -.فوائد الحديث
An shar'antawa dukkan wanda ya farka daga bacci ya face hanci dan gusar da gurbin Shaiɗan daga hancinsa, idan ya kasance zai yi alwala, to umarnin ya fi ƙarfafuwa a lokacin.
Face hanci yana daga cikar fa'idar shaƙa ruwa; domin shaƙa ruwa tsarkake cikin hanci ne, facewa kuma hakan yana fitar da datti tare da ruwan.
Ƙayyade shi da baccin dare, dan yin riƙo daga lafazin "yana kwana"; domin kwana ba ya kasancewa sai daga baccin dare, kuma cewa shi ne lokacin zatan tsawaitawa da zirfafawa.
A cikin hadisin akwai dalili akan cakuɗuwar Shaiɗan ga mutum alhali shi ba ya jin hakan.
التصنيفات
Sifar Al-wala