: :

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi ya ce: Yana daga cikin sunnah idan mai kiran sallah a kiran sallar Asuba ya ce: Hayya alal falah (Ku yi gaggawa zuwa tsira), to ya ce: Assalatu khairun minan naum (Sallah ta fi bacci alheri).

[Ingantacce ne] [Ibn Khuzaimah ya rawaito shi - Al-Baihaki ne Ya Rawaito shi - Al-Dar Al-Kutni Ya Rawaito shi]

الشرح

Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya bada labari, cewa daga abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tabbatar da shi a cikin sunnarsa, shi ne mai kiran sallah ya ce a cikin kiran sallar Asuba kadai, bayan faɗinsa: (Hayya alal falah (ku yi gaggawa zuwa tsira)), ya ce: (Assalatu khairun minan naum (sallah tafi bacci alheri)).

فوائد الحديث

Faɗinsa:

(Yana daga sunnah): Yana nufin sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, to shi yana da hukuncin Raf'u, wato wanda aka danganta shi zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

An so mai kiran sallah a cikin kiran sallar Asuba ya ce bayan ya faɗi: Hayya alal falah (ku yi gaggawa zuwa tsira): Assalatu khairun minan naum (Sallah ta fi bacci alheri), sau biyu; domin sallar Asuba a lokacin da mutane suke bacci ne a cikinsa, zasu tashi daga bacci zuwa sallah, sai aka keɓanci sallar Asuba da hakan banda sauran sallolin.

التصنيفات

Kiran Sallah da Iqama