'Lallai waɗannan sallolin biyu sune mafi nauyin salloli akan munafuki, da kun san abinda ke cikinsu da kun zo musu koda da jan ciki ne akan gwiwowi

'Lallai waɗannan sallolin biyu sune mafi nauyin salloli akan munafuki, da kun san abinda ke cikinsu da kun zo musu koda da jan ciki ne akan gwiwowi

Daga Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallar Asuba wata rana sai ya ce: "Shin wane ya zo ne?" suka ce: A'a, ya ce: "Shin wane ya zo ne?" Suka ce: A'a, ya ce: 'Lallai waɗannan sallolin biyu sune mafi nauyin salloli akan munafuki, da kun san abinda ke cikinsu da kun zo musu koda da jan ciki ne akan gwiwowi, kuma cewa sahun farko yana kan kwatankwacin sahun mala'iku, da ace kun san falalarsa da kun yi gaggawarsa. Lallai sallar namiji tare da namiji tafi tsarki daga sallarsa shi kaɗai, kuma sallarsa tare da maza biyu tafi tsarki daga sallarsa tare da namiji ɗaya, abinda ya yawaita to shine mafi soyuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -".

[Ingantacce ne] [Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi sallar Asuba wata rana, sannan ya yi tambaya: Shin wane ya zo wannan sallar da muka yi? Sahabbai suka ce: A'a. Sannan ya ce: Shin wane ya zo ne? ga wani mutumin daban, Suka ce: A'a. (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Lallai sallar Asuba da Issha'i sune mafi nauyin salloli akan munafukai; dan rinjayar kasala a cikinsu, da kuma ƙarancin faruwar riya garesu, tunda ba'a ganinsu a cikin duhu. Da kun san yaku muminai abinda ke cikin sallolin Asuba da Issha'i na lada da sakamako mai ƙaruwa - domin lada yana kan gwargwadan wahala - da kun zo su koda da jan ciki ne da tafiya akan hannaye da gwiwowi. Kuma masu sahu na farko a kusancinsu da liman kamar sahun mala'iku ne a kusancinsu ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da muminai suna sanin abinda ke cikin falalar sahun farko da sun yi tsere gare shi . Kuma lallai sallar namiji tare da namiji ita ce mafi girman sakamako da tasiri a sallarsa shi kaɗai, kuma sallarsa tare da maza biyu tafi tare da namiji ɗaya, Sallar da masallatan suka yi yawa a cikinta ita ce mafi soyuwa ga Allah kuma ta fi lada.

فوائد الحديث

Halaccin limamin masallaci ya bibiyi halayen mamu, da tambaya daga wanda ya bai zo ba daga cikinsu.

Lazimtar sallar jam’i musamman ma dai sallar Issha'i da Asuba yana daga alamomin imani.

Girman ladan sallolin Issha'i da Asuba; dan abinda ke cikin zuwa gare su na yaƙar zuciya da nacewa akan ɗa'a, sai ladansu ya zama mafi girma daga wasunsu.

Sallar jama'a tana ƙulluwa ne daga mutum biyu zuwa sama.

Bayanin falalar sahun farko, da kwaɗaitarwa a cikin gaggawa zuwa gare shi .

Falalar yawan jama'a, domin cewa duk lokacin jama'a suka yi yawa ladan yafi yawa.

Ayyuka na gari suna da fifikon lada gwargwadan fifitawar shari'a garesu, da kuma abinda suka siffantu da su na halaye.

التصنيفات

Falalar Sallah cikin jama’a da Hukunce Hukuncenta