Ban taɓa ganin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana ƙyaƙyata dariya ba, har inga ƙarshen ganɗarsa ba, kawai ya kasance yana murmushi

Ban taɓa ganin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana ƙyaƙyata dariya ba, har inga ƙarshen ganɗarsa ba, kawai ya kasance yana murmushi

Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Ban taɓa ganin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana ƙyaƙyata dariya ba, har inga ƙarshen ganɗarsa ba, kawai ya kasance yana murmushi.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai zama mai kai matuƙa a dariya ba har aga ganɗarsa ta sama ba, ita ce naman dake rataye a saman maƙogwaro, kawai ya kasance yana murmushi ne.

فوائد الحديث

Dariyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance murmushi ce idan ya yarda da wani abu ko aka ƙayatar da shi da wani abu.

Ibnu Hajar ya ce: Ban taɓa ganinsa ba yana ƙyaƙyata dariya ba ta inda zai tayin dariya cikakkiyar dariya mai fuskantowa da gabadayansa akan dariya ba.

Yawaita dariya da ɗaga murya da ƙyaƙyata dariya bai zama daga siffofin mutanen kirki ba.

Yawaita dariya yana tafiyar da kwarjinin mutum da kuma nutsuwarsa a tsakanin 'yan uwansa.

التصنيفات

Dariyarsa SAW