Idan bawa musulmi ya yi alwala - ko kuma mumini - sai ya wanke fuskar sa, to kowane kuskuren da ya yi kallo da shi da idanun sa zai fice daga fuskar sa tare da ruwa - ko kuma tare da ƙarshen ɗigon ruwa

Idan bawa musulmi ya yi alwala - ko kuma mumini - sai ya wanke fuskar sa, to kowane kuskuren da ya yi kallo da shi da idanun sa zai fice daga fuskar sa tare da ruwa - ko kuma tare da ƙarshen ɗigon ruwa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan bawa musulmi ya yi alwala - ko kuma mumini - sai ya wanke fuskar sa, to kowane kuskuren da ya yi kallo da shi da idanun sa zai fice daga fuskar sa tare da ruwa - ko kuma tare da ƙarshen ɗigon ruwa - idan ya wanke hannayen sa, kowane kuskure zai fita daga hannayen sa waɗanda hannayen sa suka damƙa tare da ruwa - ko tare da ƙarshen ɗigon ruwa -, idan ya wanke ƙafafuwan sa kowane kuskuren da ƙafafuwan sa suka tafi gare shi zasu fita tare da ruwa - ko tare da ƙarshen ɗigon ruwa - har sai ya fita tsarkakakke daga zunubai".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa idan musulmi ko mumini ya yi alwala sai ya wanke fuskarsa a cikin alwalar duk ƙaramin kuskuren da ya kalla da idanuwansa zai fita daga fuskarsa tare da ruwan da ya zuba bayan wankewar ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan, idan ya wanke hannayensa kowane ƙaramin kuskuren da hannayensa suka aikata shi zai fita daga hannayensa tare da ruwan ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan, idan ya wanke ƙafafuwansa kowane ƙaramin kuskuren da ƙafafuwansa suka taka (zuwa gare shi) zai fita tare da ruwan ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan har sai ya fita tsarkakke daga ƙananan zunubai idan ya gama alwalar.

فوائد الحديث

Falalar kiyayewa akan alwala, kuma cewa ita tana kankare zunubai.

Daga shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi yana kwaɗaitar da mutane a cikin ayyukan ɗa'a da kuma ibadu ta hanyar ambatan lada da sakamako akan su.

Kowace gaɓa daga gaɓɓan mutum tana faɗawa cikin wani abu daga saɓo, saboda haka zunubai suke bin kowace gaɓar da ta aikatasu, kuma suna fita daga kowace gaɓar da ya tuba daga gareta.

Alwala, a cikinta akwai tsarkaka ta gani ɓaro-ɓaro, kuma tana kasancewa ne a lokacin da kake wanke gaɓɓan alwala, da kuma tsarkakewa ta ma'ana tana kasancewa ne daga zunuban da suka faru daga gaɓɓan.

التصنيفات

Alwala, Falalar Ayyukan Gavvai